Ana sa ran gurfanar da matasan a gaban kuliya domin su fuskanci hukunci. Hoto/Reuters

Ana tuhumar wasu 'yan Nijeriya biyu da aka tasa keyarsu zuwa Amurka da laifin cin zarafin wasu yara maza a kasar, kamar yadda mai shigar da kara na kasar ya bayyana a ranar Lahadi.

Kafafen watsa labaran Amurka sun ruwaito cewa 'yan Nijeriyan biyu su ne: Samuel Ogoshi, mai shekara 22 da Samson Ogoshi, mai shekara 20, 'yan asalin jihar Legas da ke kudancin kasar.

Matasan za su gurfana a gaban Kotun Tarayyar Amurka a birnin Grand Rapids da ke Jihar Michigan ranar Litinin, kamar yadda Babban Lauyan Gwamnatin Amurka Attorney Mark Totten ya bayyana.

Ana tuhumarsu ne da tafiyar da wata kungiyar 'yan damfara ta kasa da kasa da ke tilasta wa duk wanda ya fada tarkonsu aikata badala, inda suke fitowa a sigar mace kuma hakan ya yi sanadin mutuwar wani matashi dan shekara 17 mai suna Jordan Demay.

Matashin ya harbe kansa a ranar 25 ga watan Maris na 2022.

Kowane cikin mutanen biyu yana fuskantar laifin hadin baki wajen cin zarafin yara kanana da hadin baki wajen yada hotunan batsa da kuma bibiyar sahun mutane a intanet.

Samuel Ogoshi yana fuskantar tuhume-tuhumen cin zarafin kananan yara da ya hassada rasa rai da kuma yunkurin cin zarafin kananan yara da shi ma ya jawo asarar rai. An samu mutanen biyu da laifi ne a watan Mayu.

Kazalika ana sa ran gurfanar da mutum na uku mai suna Ezekial Ejehem Robert a gaban kuliya duk lokacin da aka kai shi Amurka.

Laifin da ake tuhumarsu da shi ya kunshi matsa wa wanda ya fada tarkonsu don ya tura musu hotunan batsa ta intanet, daga nan kuma sai su tilasta masa ya biya su wasu kudade, idan ba haka ba su ce za su wallafa hotunan a intanet duniya ta gani, ko kuma su bukaci yin wata badala da wanda ya tura musu hoton.

Babban Lauyan Gwamnatin Amurka Attorney Mark Totten ya ce "wannan mummunan laifi ne," kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Ya kara da cewa "ya kamata wadanda suke aikata wannan laifi su sani cewa za mu bi sahunsu duk inda suke a fadin duniya.

Muna kira ga wadanda suka fada tarkonsu, don Allah ku sani muna tare da ku don mu taimaka muku."

Bidiyon zaman kotun farko da aka nada bai nuna ko akwai wani lauya da ke kare mutanen biyu ba.

TRT Afrika da abokan hulda