Ƙungiyar Boko Haram, wadda ta soma kai hare-haren ta'addanci a 2009, ta yi sanadin mutuwar mutum sama da 20,000. / Photo: AP

Gwamnatin Nijeriya ta soma shari'ar 'yan Boko Haram 300 da ta kama a lokuta daban-daban.

Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta'addanci ta ƙasar Michael Abu ya sanar da hakan ranar Laraba a Abuja babban birnin ƙasar.

Abu ya ce ana gudanar da shari'ar ce a wata Babbar Kotun Tarayya ta Nijeriya kuma ana bin dokokin ƙasashen duniya wajen gudanar da ita.

Ya ƙara da cewa alƙalai biyar ne suke jagoranctar shari'ar da zummar yin adalci ga mambobin na Boko Haam guda 300.

A baya gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin tuhumar mambobin Boko Haram 5,000 da aka kama a arewa maso gabashin ƙasar. Ana yi musu shari'a a wata babbar kotun tarayya ta ƙasar.

Ƙungiyar Boko Haram, wadda ta soma kai hare-haren ta'addanci a 2009, ta yi sanadin mutuwar mutum sama da 20,000.

Ƙungiyar ta faɗada hare-harenta zuwa maƙwabtan ƙasashe irin su Kamaru, Nijar da Chadi tun daga shekarar 2015, lamarin da ya kai ga kisan ƙarin mutum aƙalla 2,000 a Yankin Tafkin Chadi.

Sai dai gwamnatin Nijeriya ta ce ta kakkaɓe galibin mayaƙan ƙungiyar ta Boko Haram ko da yake sukan kai hare-hare lokaci zuwa lokaci.

Kazalika ana samun rahotanni na mayaƙan Boko Haram da ke miƙa wuya ga hukumomin tsaro tare da ajiye makamansu.

TRT Afrika da abokan hulda