Taron ya ja hankalin jama'a da dama, inda fitattun 'yan kasar Ghana suka halarcin bikin dasa itatuwan. / Hoto: Nana Akufo-Addo

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya sanar da cewa gwamnatin ƙasar ta shuka sama da bishiyoyi miliyan 42 a cikin sama da shekara uku, a yunƙurin ƙasar na kiyayewa da kyautata muhalli.

A wani saƙon da shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa “A cikin sama da shekara uku, tare da goyon bayan al’umma, an shuka sama da bishiyoyi miliyan 42 a faɗin Ghana.

A bana, wannan shirin na da zummar dasa ƙarin bishiyoyi miliyan 10, wanda hakan zai kawo jumullarsu zuwa miliyan 52 a cikin shekara huɗu.

A ranar 7 ga watan Yuni ne aka yi bikin Ranar Green Ghana. Ranar Green Ghana wani shiri ne da gwamnati ta kaddamar a shekarar 2021, da nufin yaki da sare itatuwa da kuma inganta muhalli dorewa.

Taron ya ja hankalin jama'a da dama, inda fitattun 'yan kasar Ghana suka halarcin bikin dasa itatuwan.

Shugaba Akufo-Addo ya jaddada muhimmiyar rawar da dazuka ke takawa wajen dorewar rayuwa a doron kasa da magance matsalolin sauyin yanayi.

Shugaba Akufo-Addo ya bukaci ‘yan Ghana a duk faɗin kasar — daga Axim zuwa Zebilla, Aflao zuwa Tumu, ba tare da la’akari da sana’a ba — da su rungumi dasa itatuwa, su raine su har su girma.

TRT Afrika da abokan hulda