Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce wasu masu otel-otel sun shigar da ita ƙara kotu kuma har kotun ta ba da umarnin rufe asusun banki na Hisban.
Kwamandar rundunar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa labarin a ranar Laraba.
“E, an rufe mana duka asusun bankunanmu, amma a yanzu na tura wakili ya je ya samu Antoni-Janar don ba a gaya mana laifinmu ba da kuma dalilin hakan,” a cewar Sheikh Daurawa.
Kwamandan na Hisbah ya ce an dai aika musu takardar kotu cewa “akwai wani otel da muka je muka yi kaza, kuma sai mun biya Naira 700,000, akwai wani daban da shi ma muka je, shi kuma za mu biya Naira 100,000.
“Daga nan suka ce dole sai mun biya naira 800,000 shi ne fa sai suka rufe asusun namu," ya ce.
Ya kamata a gaya mana laifin da muka yi don mu nemi lauya ya shiga cikin zancen, idan mun kasa kare kanmu sai a yi mana hukunci.”
Fitaccen Malamin ya koka cewa wannan abu da aka yi musu ya dakatar da duka ayyukansu tun da ba za su iya taba kudaden cikin asusunsu ba.
Sheikh Daurawa ya ce idan har wasu suna ganin sun fi ƙarfin doka to su bai kamata a taɓa musu asusun banki ba
A kwanakin baya ne wani samame da rundunar Hisbah ta kai wasu otel-otel da wuraren shaƙatawa a Kano ya jawo ce-ce-ku-ce sosai.
Wasu sun yi ta yabon Hisbah kan lamarin yayin da wasu suka dinga zarginta d yin kutse da "cin mutuncin" mutane ta hanyar kama "waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.
Sai dai a lokacin Hisbah ta ce sai da ta yi bincikenta tsaf ta tattara bayanai kafin ta kai samamen, don haka "masu laifi kawai ta kama."