South Sudan's national police said in a statement on January 20, 205: "Sixteen Sudanese foreign nationals were reported killed in four states." / Photo: Reuters

Rundunar ‘yan sandan Sudan ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an kashe ‘yan kasar Sudan 16 a tarzomar da ta barke a makon da ya gabata saboda zargin kisan gillar da aka yi wa ‘yan Sudan ta Kudu a yankin Al Jazirah na kasar Sudan.

A ranakun Alhamis da Juma'a ne rikicin ya ɓarke a Juba babban birnin Sudan ta Kudu da kuma wasu wurare na ƙasar, inda masu zanga-zangar suka fusata kan abin da suka yi imani cewa da hannun sojojin Sudan da ƙungiyoyin ƙawayenta wajen kashe-kashen Al Jazirah.

Rundunar sojin Sudan ta yi Allah-wadai da abin da ta kira ‘’cin zarafi na ɗaiɗaikun mutane’’ a birnin Al Jazira bayan ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun ɗora alhakin hare-haren na ƙabilanci a kan fararen hula da ake zargi da tallafa wa 'yan tawayen rundunar RSF.

A cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan Sudan ta Kudu ta fitar, ta ce ‘’an kashe 'yan Sudan 16 a jihohi hudu.’’

Dokar hana fitar dare

‘Yan sanda za su ci gaba da sintiri a kasuwanni da wuraren zaman jama’a domin al’ummar Sudan, a cewar sanarwar.

A ranar Juma'a ne, gwamnati ta kafa dokar hana fitar dare zuwa safiya, wacce har yanzu take aiki.

Aƙalla mutane 24 ne aka kama kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike, in ji rundunar sojin Sudan ta Kudu a wata sanarwa ta daban da ta fitar.

TRT Afrika