Adadin waɗanda suka rasu a Nijeriya sakamakon bindigar da tankar mai ta yi a Dikko Junction da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja a Jihar Neja ya kai 86, inda 55 suka jikkata kuma suke samun kulawa ta likitoci, kamar yadda hukumomin ƙasar suka tabbatar a ranar Lahadi.
Abdullahi Baba-Arah, wanda shi ne darakta janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, shi ne ya bayar da sabbin alƙaluman, inda ya ƙara da cewa akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su an binne su a cikin ƙabarin bai ɗaya.
“Jumullar mutum 86 ne aka tabbatar sun rasu, inda aka gano gawawwakinsu sannan aka binne su.
“An binne mutum 80 a cikin ƙabari guda na ɓai daya a harabar Dikko Pimary Healthcare Centre, biyar kuma iyalansu ne suka karɓe su domin su binne su, ɗaya kuma ya rasu a Dikko Pimary Healthcare Centre,” in ji Baba-Arah.
Tankar ta yi bindiga ne a daidai lokacin da mutanen wurin suka yi ƙoƙarin kwalfar man fetur ɗin cikinta da ke tsiyaya, lamarin da ya halaka waɗanda suka je ɗibar man.
Ana yawan samun fashewar tankar mai bayan ta yi hatsari a Nijeriya inda jama'a da dama da ke zuwa kwalfar man fetur ke mutuwa.
Ko a kwanakin baya sai da fiye da mutum 100 suka rasu a gobarar tankar mai a Jigawa.