Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya ba da umarnin ƙaddamar da bincike kan harbe-harben da aka yi tsakanin wasu masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da sojoji a mahaƙar zinarin Anglo Gold Ashanti inda aka rasa rayuka takwas.
Shugaban ya bayar da umarni a gudanar da bincike domin hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Rahotanni daga Ghana sun ambato mai magana da yawun shugaban, Felix Ofosu-Kwakye yana cewa: “Gwamnati na nuna alhininta game da rayuka takwas da aka rasa na masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba bayan arangama a wata mahaƙar ma’adinai a Obuasi.”
Ofosu-Kwakye, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, ya ƙara da cewa “a matsayin martani ga lamarin, Shugaba Johan Dramani Mahama ya ba da umarnin gabatar da bincike nan-take domin gano yanayin da ya janyo arangamar da kuma tabbatar da cewa an hukunta duk mahalukin da ya saɓa wa doka.”
Sai dai kuma gwamnatin ƙasar ta nemi kamfanin haƙar ma’adinai na Anglo-Gold Ashanti ya ɗauki nauyin jinyar waɗanda suka ji rauni a arangamar tare da ɗaukar nauyin jana’izar waɗanda suka mutu sakamakon lamarin.
“Kuma an umarci jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin tabbatar da tsaro a yankin tare da aiwatar da matakan da za su hana aukuwar sake faruwar lamarin,” in ji shi.
Rundunar sojin ƙasar Ghana dai ta ce lamarin ya auku ne a lokacin da masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba 60 suka shiga mahaƙar ma'adinan ta katangar tsaronta.