Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta ce an kashe jimillar mutane 214 sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda, da rikicin kabilanci da fadan ramuwar gayya.
A wani sabon rahoto kan sha'anin tsaro na shekarar 2022, da kuma na watanni ukun farkon 2023 da ta fitar ranar Laraba, gwamnatin ta ce an yi kashe-kashen ne tsakanin watan Janairu da na Maris din wannan shekarar.
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya gabatar da rahoton a zauren Majalisar Tsaro ta jihar Kaduna, wadda Gwamna Nasir Ahmed Elrufai ya jagoranta.
Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu, akwai maza 196, da mata 14, da kuma kananan yara hudu, in ji rahoton.
Ya kara da cewa yankin Kaduna ta tsakiya shi ya fi yawan wadanda suka halaka, da adadin mutane 115.
Kazalika rahoton ya ce masu garkuwa da mutane sun sace mutane 746 a jihar a cikin watannin uku.
Rahoton ya bayyana cewa mutum 1,052 sakamakon hare-haren ta'addanci da na kabilanci da kuma ramuwar gayya a jihar ta Kaduna a 2022.
Jihar Kaduna tana cikin jihohin Nijeriya masu fama da rikice-rikice, kama daga ta’addanci, da fashin daji, da garkuwa da mutane, da fadan kabilanci da na addini.
Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya jaddada himmatuwar gwamnatinsa wajen inganta harkar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Haka kuma, gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta karfafa ayyukan samar da tsaro a jihohin da ke fuskantar matsalar su bakwai, wadanda ke arewa masu yamma, da kuma jihar Neja ta tsakiyar kasar.