Wani yunƙurin fasa gidan yari mafi girma a ƙasar Kongo da ke babban birnin Kinshasa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 129, mafi yawansu sun mutu saboda turmutsutsu.
Wani binciken farko da aka gudanar ya nuna an harbe fursunoni 24 sakamakon harbin gargaɗi da aka yi a yayin da suke ƙoƙarin guduwa daga gidan kurkukun Makala da ke Kinshasa a ranar Litinin, in ji Ministan Harkokin Cikin Gidan Kongo Jacquemin Shabani a wata sanarwa da ya fitar ta shafin X.
"Akwai wasu mutanen 59 da suka jikkata kuma ake kula da su a asibiti, an kuma yi wa wasu mata fyaɗe," in sji shi, yana mai ƙara da cewa al'amura sun koma daidai a gidan kurkukun d aka kona wani ɓangare nasa a yayin kai harin.
Makala, gidan kurkuku mafi girma a Kongo da ke kula da mutane 1,500, amma aka cika shi da fursunoni 12,000, mafi yawan su waɗanda ke jiran a yanke musu hukunci, kamar yadda Ƙungiyar Kare Hakkokin Ɗan'Adam ta Amnesty International a rahotonta na shekarar da ta gabata. A baya ma an sha fasa gidan yarin, ciki har da na 2017, inda wata ƙungiyar addini ta kuɓutar da mambobinta.
Makirci a cikin kurkukun
Tun a talatainin daren Lahadi ne aka fara jin harbe-harbe har zuwa safiyar Litinin a gidan kurkukun, in ji wani mazaunin yankin. Tun da fari wani babban jami'in gwamnati ya sanar da cewa mutuwar mutane biyu kawai aka tabbatar yayin harin, adadin da masu kare hakkokin ɗan'adam suke da jayayya a kai.
Bidiyon da ka samu na nuna gawarwaki kwance a gidan kurkukun, mafi yawansu na ɗauke da raunuka. Wani bidiyon kuma ya nuna yadda furunoni suke ɗaukar waɗanda suka mutu suke saka su a cikin mota.
Babu wata alama ta yunƙurin shiga kurkukun da ƙarfi da yaji da aka samu. Gidan kurkukun na da nisan kilomita 5 daga fadar shugaban ƙasa a babban birnin Kinsasha.
Wasu fursunoni da ke cikin gidan yarin ne suka fara yunƙurin tserewa daga kurkukun, in ji Mbemba Kabuya, mataimakin ministan shari'a a tattaunawar da ya yi da tashar FM mafi girma a Kongo.
Zagon ƙasa
Awanni bayan kai harin, an rufe dukkan hanyoyin da ke zuwa gidan yarin inda mahukunta suka kafa kwamitin bincike kan lamarin.
Makala - tare da wasu gidajen kurkuku a Kongo- sun cika da fursunoni da yawa inda mafi yawan su suke mutuwa saboda yunwa, in ji masu fafutu. An saki wasu fursunoni a wannan shekarar.
Ministan hari'a Constant Mutamba ya kira harin da "zagon ƙasa da aka shirya yi", yana mai ƙarawa da cewa "waɗanda suka kitsa zagon ƙasa za su fuskanci martani marar daɗi."
Ya kuma sanar da haramta ɗauke fursunoni daga gidajen kurkuku inda ya ce mahukunta za su gina sabbin gidajen kurkuku.