Aly Benjamin Coulibaly ya ce ya samu rahotanni kai hare-hare a ƙauyukan Komsilga, Nodin da kuma Soroe da ke lardin Yatenga ranar 25 ga watan Fabrairu./Hoto: Reuters

Mutum kusan 170 ne suka mutu a wasu hare-hare da masu tayar da ƙayar baya suka kai a ƙauyuka uku a arewacin Burkina Faso a makon da ya wuce, a cewar wani mai shigar da ƙara na gwamnatin ƙasar a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.

Aly Benjamin Coulibaly ya ce ya samu rahotanni na kai hare-hare a ƙauyukan Komsilga, Nodin da Soroe da ke lardin Yatenga ranar 25 ga watan Fabrairu, inda alƙaluman wucin gadi suka nuna cewa "an kashe kusan mutum 170".

Kazalika mutane da dama sun jikkata sannan maharan sun lalata wurare, a cewar mai shigar da ƙarar na garin Ouahigouya da ke arewacin ƙasar.

Ya ce ofishinsa ya bayar da umarni a gudanar da bincike kuma ya yi kira ga jama'a su bayar da bayani kan yadda za a gano maharan.

Mutanen da suka tsira daga hare-haren sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mata da yara ƙanana suna cikin waɗanda aka kashe.

Jami'an tsaro sun ce hare-haren sun bambanta da waɗanda aka kai a wani masallaci da watancoci a arewacin Burkina Faso a makon jiya.

Har yanzu hukumomi ba su fitar da alƙaluman mutanen da aka kashe a waɗancan hare-haren ba.

Burkina Faso ta daɗe tana fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi waɗanda ke da alaƙa da Al-Qaeda da IS inda kuma suke kai hari a Mali da ke maƙwabtaka tun 2015.

AFP