Rundunar Sojin Ƙasa a Nijeriya ta ce ta tsare wani jami'inta da ya harba bindiga don gargaɗi ga masu zanga-zanga a garin Zaria na jihar Kaduna, inda harsashin ya samu wani yaro tare da halaka shi.
A wata sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba, ta bayyana cewar a ranar 6 ga Agusta Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta samu kiran neman agaji saboda wasu ɓata-gari sun taru a Samaru, suna ƙona tayoyi a kan hanya da jifan jamia'n tsaro da duwatsu.
Hakan ne ya sa rundunar ta tura jami'anta zuwa wajen da niyyar tarwatsa ɓata-garin da kuma tabbatar da an bi dokar hana fita da gwamnatin Jihar Kaduna ta saka.
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan zuwan sojoji wajen, ɓata-garin suka yi yunƙurin kai musu hari, abin da ya sanya wani soja harba bindiga don gargaɗinsu, amma tsautsayi ya sanya harsashin ya faɗa kan wani yaro ɗan shekara 16 mai suna Ismail Mohammed wanda ya kuma rasu.
"Bayan bayyana matuƙar ɓacin rai game da lamarin, Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa Laftanal Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ya aike da babbar tawaga ƙarƙashin Babban Kwamandan Runduna ta 1 Manjo Janar Lander Saraso don yin ta'aziyya ga iyayen yaron da aka kashe," in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ce tuni aka tsare tare da fara binciken sojan da ya yi harbin
Zanga-Zangar neman kawo ƙarshen mummunan jagoranci
Tun ranar 1 ga Agusta ne 'yan Nijeriya a garuruwan ƙasar daban-daban suka fara gudanar da zanga-zangar adawa da tsarin shugabanci mara kyau da suke cewar ana yi a ƙasar, inda suka ce yunwa da talauci sun yi musu katutu.
Masu zanga-zangar a garuruwa da dama sun dinga fasa kantuna da gine-ginen gwamnati inda suke satar kayayyakin jama'a da ɓarnata dukiyoyi.
Jami'an 'yan sanda sun kama ɗaruruwan masu zanga-zangar da aka ce ta lumana ce amma ta rikiɗe zuwa tarzoma, inda tuni aka aika da galibinsu gidajenn gyaran hali, za kuma su gurfana a gaban ƙuliya.
Za mu kama masu ingiza zanga-zanga daga wajen Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewar tana sanya idanu kan wasu 'yan ƙasar da ke ƙasashen waje kuma suke ingizawa da ɗaukar nauyin zanga-zangar neman kawo ƙarshen mummunan shugabanci a ƙasar.
Shugabar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya Kemi Nandap ta ce ana sanya idanu kan idanu kan masu ɗaukar nauyin zanga-zangar, kuma da zarar sun shiga ƙasar za a kama su.
A yayin wani taron manema labarai da dukkan shugabannin hukumomin tsaron Nijeriya suka gudanar ranar Talata a Abuja, Misis Nandap ta sha alwashin kama waɗannan mutane da ke ƙasashen waje saboda ingiza masu zanga-zangar.
"Mun gano wasu masu ɗaukar nauyin zanga-zanga a ƙasashen waje; muna sanya idanu a kan su," in ji shugabar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya.
Nandap ta ƙara da cewar sun kai ƙarin ma'aikata kan iyakoki da filayen jiragen saman Nijeriya, sannan suna aiki don tabbatar da ganin babu wata ƙasar waje da ta yi kutse don taimaka wa masu zanga-zanga a Nijeriya.
Ana bincikar wasu manyan 'yan siyasa da hannu a ɗaga tutar Rasha
Jami'an tsaron Nijeriya sun bayyana fara bincike kan wasu manyan 'yan siyasa a arewacin ƙasar su huɗu bisa zargin hannu a ɗaga tutar Rasha a yayin zanga-zangar.
Jaridun Nijeriya sun rawaito cewar an fara binciken manyan 'yan siyasar da suka fito daga jihohin Kaduna, Kano da Katsina kan lamarin.
Sai dai ba a bayyana sunayensu ba, ko da yake wasu bayanai sun ce mutanen sun taka muhimmiyar rawa a lokacin babban zaɓen 2023.