Hukumar Tsaron Ƙasa ta Ghana ta ce ta kama takardun kuɗi na dalar Amurka da Cedi da zinari na jabu da aka ɓoye cikin kwantenoni na dakon kaya.
Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ambato wata sanarwar da Hukumar Tsaron Ƙasa ta fitar wadda ke cewa jami’anta sun bi sawun kwantenonin ne zuwa wani ɗakin ajiya a unguwar Ofanko a ƙaramar hukumar Ga South a Accra bayan an tsegunta musu lamarin.
Sanarwar ta ce kuɗaɗen da aka ɓoye ɗin, yawancin su dalolin Amurka ne da aka samu cikin akwatunan katako cike da siminti.
Ta ƙara da cewa sauran akwatunan da aka buɗe a lokacin samamen sun nuna ƙarin takardun kuɗaɗe da aka rufe da gawayi.
Sanarwar ta ce, jami’an Hukumar Tsaron da suka yi kamen sun ce har yanzu ba su gano kwantenoni biyu ba, amma sun duƙufa wajen nemo su.
Kazalika an fara neman waɗanda ake zargi da hannu a aika-aikar ciki har da wani mutum da ake ce wa Alhaji.
“An gano ababen tayar da hankali a ɗakin, ciki har da akwatuna ɗauke da ƙarafunan da ake tsammani zinari ne da takardun ƙuɗaɗen Cedi na Cedi 50 da Cedi 100 da kuma kayan soji ta takalman bogi,” in ji sanarwar.