Rundunar 'yan sandan ta ce tana sane da munanan ayyukan ƙungiyar asirin na kisan mutane a manyan makarantu da faɗace-faɗace a tsakanin ƙungiyoyin asiri da tayar da zaune-tsaye da sauran manyan laifuka./Hoto:Rundunar 'yan sandan Nijeriya

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ja hankalin 'yan ƙasar game da shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi a faɗin ƙasar musamman a jami'o'i da manyan makarantu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Ribas Grace Iringe-Koko ce ta yi wannan jan hankali a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar da maraice a birnin Fatakwal.

Ta bayyana cewa wata babbar ƙungiyar asiri ta Nijeriya tana shirin gudanar da gagarumin biki ranar Lahadi a faɗin Nijeriya, musamman a jami'o'i don tunawa da mutumin da ya kafa ta.

"Rundunar 'yan sandan Jihar Ribas ta samu bayanai game da bikin da ƙungiyar Neo-Black Movement (NBM) za ta yi a faɗin ƙasar ranar 7 ga watan Yulin 2024. Ƙungiyar, wadda ake yi wa laƙabi da Aiye ko Black Axe, tana shirin gudanar da bikin ne domin tunawa da wanda ya kafa ta.

Bikin, wanda aka sanya wa suna Ranar AIYE ko 7/7 za a gudanar da shi ne a dukkan jihohin da ke faɗin ƙasa, musamman a manyan makarantu," in ji sanarwar.

Rundunar 'yan sandan ta ce tana sane da munanan ayyukan ƙungiyar asirin na kisan mutane a manyan makarantu da faɗace-faɗace a tsakanin ƙungiyoyin asiri da tayar da zaune-tsaye da sauran manyan laifuka.

Ta ce yanzu haka ta baza ƙarin jami'an 'yan sanda zuwa wasu wurare domin daƙile ayyukan ƙungiyoyin asiri, sannan ta yi kira ga iyaye su gargaɗi 'ya'yansu su guji shiga ayyukan ƙungiyoyin asiri.

"Ana bai wa manyan makarantu shawarar ƙara matakan tsaro da kuma sanya idanu sosai domin tabbatar da tsaron dukkan ɗalibai. Kazalika ana kira ga dukkan makarantu su lura da duk wani taro na ɗalibai da bai kwanta musu a rai ba," a cewar sanarwar.

TRT Afrika