Rahotanni daga Zamfara Jihar da ke arewa maso yammacin Nijeriya na cewa dalibai mata da 'yan bindiga suka sace kusan watanni biyu da suka wuce sun shaki iskar 'yanci.
Gidan talabijin na Nigeria Television Authority, NTA, ya rawaito cewa daliban guda biyar, wadanda aka sace daga Jami'ar Tarayya da ke Gusau babban birnin jihar, sun isa hannun iyayensu.
Sai dai bai fadi yadda daliban suka kubuta ba da kuma lokacin da aka yi hakan.
Amma wani sako da ya wallafa a shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter, ya ambato babban jami'in da ke hulda da dalibai na Jami'ar, Dr Lawal Sa'ad yana cewa sojoji ne suka mika musu daliban.
"Ya ce an duba lafiyar daliban da aka sako kuma tuni aka mika su ga iyayensu," in ji NTA.
Zamfara na fama da hare-haren 'yan bindiga da ke sace dalibai da mutanen gari domin karbar kudin fansa. A lokuta da dama suka kashe mutanen da suka sace.
A watan Fabrairun 2021 ne 'yan bindiga suka sace dalibai mata 279 daga makarantar sakandare ta mata da ke Jangebe, lamarin da ya ja hankalin duniya.