Rundunar 'yan sandan duniya ta Interpol ta ce ta kwace €2.15m ($2.3m) daga 'yan damfarar intanet da ke da cibiya a Yammacin Afirka sannan ta kama fiye da mutum 100 a samamen da ta kai a kasashe daban-daban.
Ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ranar Talata.
Interpol ta ce ta gudanar da samamen ne, wanda ta yi wa lakabi da “Operation Jackal,” daga ranar 15 zuwa ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023.
A cewar rundunar ta rufe asusan bankuna da dama sannan ta kaddamar da jerin bincike kan gungun 'yan damfara a Yammacin Afirka irin su kungiyar Black Axe da ke Nijeriya.
Wannan lamari ya “sanya mun gano wadanda ake zargi fiye da 1,100, an kama mutum 103 sannan aka rufe asusan bankuna fiye da 200 da ke da alaka da damfarar intanet,” in ji sanarwar ta Interpol,
'Yan sanda da jami'an hukumomin yaki da damfarar intanet na kasashe 21 daga sassan duniya ne suka sanya hannu a wannan aiki, wanda ya ka ga kama “manyan 'yan damfarar intanet da dama da ke yin barazana ga tsaron lafiyar duniya."
Rundunar ta ce: “Hakan ya aike da kwakkwaran sako ga 'yan damfarar intanet da ke Yammacin Afirka cewa Interpol za ta tunkare su ta kowace hanya duk buyan da suka yi a intanet."
Interpol za ta ci gaba da mayar da hankali kan haramtattun ayyuka na Black Axe da sauran gungun kungiyoyin da ke aikata laifuka a shafin intanet,” a cewar sanarwar, wadda Isaac Kehinde Oginni, daraktan da ke sanya ido kan haramtattun harkokin kudi da laifukan intanet na rundunar, ya fitar.