Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta'annati, EFCC, ta ce jami'anta sun kama mutane da dama da ake zargi da yin damfara ta intanet a Enugu da ke kudu maso gabashin kasar.
Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafukanta na soshiyal midiya ranar Juma'a ta ce jami'anta da ke Enugu sun kama "mutum 33 da ake zargi da yin damfara ta intanet a wani samame" da suka kai musu.
Ta kara da cewa an kama mutanen ne ranar 20 ga watan Yuni.
Mutanen da aka kama su ne:
Micheal Ogobodo
Michael Elijah
Sopuluchukwu Michael
Michael Joshua
Ogu Jerry
Ebuka Okafor
Ehinyameh Eromosele
Emeka Okongwu
Jane Ogwunga
Okpara Chidera
Emmanuel Abah
David Okwo
Chidozie Okpara
Ngene Samuel
Onuh Kelvin Uchechukwu
Ebuka Kalu Bewell
Oba Stanley Ikechukwu
Kalu Chukwudalu
Ifeanyi Jeff Ukwuoma
Paschal Ugwuanyi
Chukwuma Peter
Ukwuoma Nmasi Joseph
Obiozor Franklin
Chimaobi Kelvin Azubuike
Okafor Damian
Kulugh Simio
Okafor Ifeanyi Gabriel
Ugochukwu Nnabife
Godwin Ifeanyi
Henry Chima
Arinze Ogu
Emmanuel Peter
Godwin Miracle
Hukumar ta EFCC ta ce ta kwato abubuwa da dama daga hannunsu da suka hada da motocin alfarma hudu, wayoyin salula 49, konfuta bakwai, na'urar ajiye bayanan komfuta wato Flash drive da ya da kuma fasfo guda daya.
Ta kara da cewa mutanen da ake zargi sun yi magana kan abubuwan da ake tuhumarsu da aikatawa kua za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
Damfara a intanet wani batu ne da ke neman zama ruwan dare a Nijeriya inda galibin masu yinsa suke sace makudan kudade daga hannun jama'a, ciki har da 'yan kasashen waje.