Mmesoma Ejikeme: Kamfanin motoci na Innoson ya kwace tallafin karatun da ya bai wa dalibar

Mmesoma Ejikeme: Kamfanin motoci na Innoson ya kwace tallafin karatun da ya bai wa dalibar

Kamfanin kera motocin ya ce ya kwace tallafin naira miliyan uku da ya bai wa matashiyar ne saboda ba ya goyon bayan rashin gaskiya.
Mmesoma Ejikeme ta yi karyar cewa ta samu maki 362 a jarrabawar JAMB./Hoto:OTHER

Kamfanin kera motoci na Innoson Vehicles da ke Nijeriya ya kwace tallafin karatun da ya bai wa matashiyar nan Mmesoma Ejikeme da ta shirga karya a sakamakon jarrabawarta ta share fagen shiga makarantun gaba da sakandare, wato JAMB.

Ejikeme, ‘yar asalin jihar Anambra mai shekara 19, ta yi ikirarin samun maki 362, lamarin da ya sa ta zama daliba mafi kwazo a jarrabawar a shekarar 2023.

Hakan ne ya sa kamfanoni da daidakun jama’a suka rika yi mata kyauta, ciki har da kyautar N3m da attajirin nan mai kamfanin kera motoci, Innocent Chukwuma, ya ba ta a matsayin tallafin karatu.

Amma a baya bayan nan takaddama ta kaure game da sahihancin sakamakon jarrabawarta, lamarin da ya sa hukumar da ke shirya jarrabawar shiga manyan makarantu a Nijeriya ta karyata ikirarin dalibar cewa ta samu maki mafi yawa a jarrabawar JAMB.

Tun da farko dai dalibar da mahaifinta sun nace cewa sakamakon nata na gaskiya ne.

Sai dai bayan wani bincike da gwamnatin jihar Anambra ta gudanar ya tabbatar da cewa matashiyar ta shirga karya, mahaifinta ya nemi gafarar JAMB da 'yan Nijeriya.

Mr Romanus Ejikeme ya bayyana cewa 'yarsa ta yi masa karya game da sakamakon jarrabawarta.

Hakan ya sa mutanen da suka bai wa matashiyar tallafin karatu irin su Innoson Vehicles suka kwace kudadensu.

Saba ka’ida

Kamfanin ya ce ya kwace tallafin da ya bai wa dalibar ne domin “tsare gaskiya” bayan binciken da bangarori daban-daban suka yi ya gano cewa Mmesoma ta yi karya a sakamakon jarrabawarta.

“Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa Miss Joy Mmesoma Ejikame ta jirkita sakamakon jarrabawarta ta UMTE. Wannan abin takaici ne matuka kuma ya saba wa ka’idojinmu na Innoson Vehicles.

"Bisa wadannan ka’idoji da kuma sakamakon bincike, mun dauki mataki mai wahala na karbe tallafin karatun da muka bai wa Miss Joy Mmesoma Ejikeme," in ji sanarwar da kamfanin ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Asabar.

TRT Afrika