Ana zargin cewa littafin na yada manufofin 'yan luwadi:Hoto/Facebook/Abba Almustapha

Shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Dab'i ta Kano a Nijeriya, Abba El-Mustapha, ya ce hukumar ta haramta karantawa da sayar da littafin Queen Primer a fadin jihar.

Ya bayyana haka ne ranar Alhamis a yayin da ya jagoranci kwace kwafi-kwafi masu dimbin yawa na littattan.

Littafin yana dauke da wasu kalaman turanci irin su 'let's gay' wato 'mu shakata', sai dai wasu na ganin amfani da kalmar 'gay' wani sako ne na lalata tarbiyyar jama'a.

El-Mustapha ya ce littafin wanda ke koyar da rubutu da karatu a harshen Ingilishin yana yada "fasadi."

"Littafin yana cike da maganganu na fasadi wadanda ba su kamata a ce 'ya'yanmu sun ji su ba kuma an karantar da su ba," in ji shi kamar yadda ya wallafa a wani bidiyo a shafinsa na Facebook.

Shugaban hukumar ya ce jami'ansa sun kama kwafin littafin guda 1,200 daga kasuwannin da ake sayar da su.

Kazalika ya ce za su ci gaba da bincike a kan al'amarin kuma ya sha alwashin gurfanar da duk wanda aka sake kamawa yana sayar da littafin a gaban kuliya.

"Matsayar wannan hukuma ita ce dakatar da sayar da wannan littafin da dangoginsa. Kuma ta hana amfani da shi a cikin [jihar] Kano gaba daya. Sannan duk wasu makarantu da ke koyar da yara wannan littafin daga yanzu mun hana. Kuma mun haramta sayar da shi gaba daya a jihar Kano," in ji Abba El-Mustapha.

Batun littafin Queen Primer ya jawo ce-ce-ku-ce a 'yan kwanakin nan musamman a kafafen sada zumunta, inda har fitaccen malamin addini a jihar, Dokta Aliyu Umar, wato Limamin Masallacin Al Furqan, ya taba yin gargadi kan sabon bugun littafin Queen Primer da ake amfani wajen koyar da harshen Turancin Ingilishi ga yara 'yan nazare da firamare.

TRT Afrika