Daruruwan ‘yan Ghana ne suka fito kan titunan birnin Accra a ranar Asabar a wata zanga-zangar lumana don nuna rashin jin dadinsu game da katsewar wutar lantarki da ke shafar harkokin kasuwanci da rayuwar yau da kullum a fadin kasar ta yammacin Afirka.
Sanye da jajaye da bakaken kaya, inda jagororin zanga-zangar suka saka jar hula, masu zanga-zangar sun zagaya cikin babban birnin kasar, suna kira ga gwamnati da ta gyara wutar lantarki.
Sun ta rera waƙoƙin kishin ƙasa da ɗaukar fitilu masu amfani da kananzir don nuna alamar halin da suke ciki. Wannan zanga-zangar ta jawo cunkoson ababen hawa a birnin.
Duk da kasancewar kasar Ghana na daya daga cikin kasashen Afirka na farko da suka fara kokarin samar da wutar lantarki, Ghana na fama da matsalar karancin lantarkin.
Shahararriyar mai shirya fina-finan nan Yvonne Nelson ce ta shirya zanga-zangar, wadda ta samu halartar fitattun mawaƙa da ‘yan fim.
Sun yi wa zanga-zangar laƙabi da #DumsorMustStop — inda dumsor ke nufin ɗauke wuta, wanda laƙabin zanga-zangar na nufin a daina ɗauke wuta.
“Ina cikin zafi, kuma na fito nan ne domin na yi ƙorafi,” kamar yadda Nelson ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Ɗan wasan barkwancin nan DKB shi ma na daga cikin waɗanda suka halarci zanga-zangar kuma ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa: "Wannan katsewar wutar lantarkin da ake yi ba tare da sanarwa ba na kashe mana sana'ar mu. Muna bukatar ingantacciyar wutar lantarki domin samun ci gaba," in ji shi.
Baya ga mawaƙan da ‘yan fim, sauran ‘yan ƙasar ta Ghana su ma sun bayyana ƙorafinsu.
Wata mai shago Anita Twumasi ta shaida cewa jaririyarta ‘yar wata shida na shan wahala duk lokacin da aka ɗauke wuta sakamakon tsananin zafi.
"Yarinyata ba za ta iya jure wa zafi ba, duk lokacin da wutar lantarki ta ɗauke, ina damuwa da lafiyarta," in ji ta.