A ranar Asabar aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Kano.
Rahotanni daga jihar na cewa tun da safe masu kaɗa ƙuri’a suka fita zaɓe a jihar domin zaɓen kansiloli da kuma shugabannin ƙananan hukumomi.
Jam’iyyu shida ne ke suka fafata a zaɓen ƙananan hukumomin, kamar yadda shugaban hukumar zaɓen ta Kano Sani Malumfashi ya tabbatar.
Jam’iyyun sun haɗa da Nigeria People Party (NNPP), Zenith Labour Party (ZLP) Accord Party (AP) National Rescue Movement (NRM), African Action Congress (AAC) da Action Alliance (AA).
Jam’iyyar APC ta sanar da ƙaurace wa wannan zaɓen. Sai dai zaɓen yana cike da tirka-tirka domin tuni Kotun Tarayyar Nijeriyar ta haramta gudanar da shi inda ta ce wasu mambobin hukumar zaɓen ta Kano KANSIEC ‘yan Jam’iyyar NNPP mai mulki ne a jihar.
Sai dai kotun jihar Kano ta yi hukunci wanda ya ci karo da na tarayya inda ita kuma ta umarci hukumar zaɓen ta Kano da ta gudanar da zaɓen a ranar Asabar.
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce babu gudu ba ja da baya wurin gudanar da zaɓen.
Ita kuma rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce za ta bi umarnin kotu, inda ta ce za ta ƙaurace wa zaɓen.
Rahotanni daga Kanon na cewa jami’an Hisbah da ‘yan Karota ne ke bayar da tsaro a rumfunan zaɓen da safiyar ta Asabar.