Hukumomin mulkin sojin Burkina Faso sun ce a ranar Laraba sun murkushe wani yunkuri da wasu sojoji da jami'an tsaro suka yi na kifar da gwamnatin kasar.
Gwamnatin rikon kwaryar kasar ta shaida wa 'yan kasar cewa "Jami'an leken asirin Burkina Faso da sauran jami'an tsaro sun dakile wani yunkurin juyin mulki da aka yi ranar 26 ga watan Satumba, 2023.”
An kama sojoji da sauran mutanen da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Kyaftin Ibrahim Traore da kuma kawo tashin hankali a kasar, in ji sanarwar da kakakin gwamnatin Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo ya fitar.
Gwamnatin ta tabbatar wa 'yan kasar cewa za ta yi musu karin haske kan abin da ya faru.
Ranar Talata da daddare, daruruwan 'yan kasar Burkina Faso suka bazama a kan titunan babban birnin kasar Ouagadougou domin nuna goyon bayansu ga gwamnatin rikon kwarya a yayin da ake watsa jita-jitar yunkurin juyin mulkin.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, shugaban kasar Ibrahim Traore ya gode wa magoya bayansa
Ya yi alkawarin shugabantar gwamnatin rikon kwarya cikin “lumana, duk da kiyayya da sukar da ake yi wa yunkurin hana neman zama kasa mai 'yanci.”
A watan Satumba na shekarar da ta gabata, Traore ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Paul Henri-Damiba, wanda shi ma juyin mulki ya yi wa shugaban Burkina Faso a watan Janairun 2022.