Ƴan bindiga a kan babura sun kashe mutum 22 a wani hari da suka kai yammacin Jamhuriyar Nijar kusa da iyakar ƙasar da Mali, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Harin wanda aka kai a ranar Lahadi, an kai shi ne a ƙauyen Motogatta da ke yankin Tillaberi wanda a nan ne iyakokin Nijar da Mali da Burkina Faso suka haɗu, inda kuma a nan ne ƴan bindiga suka daɗe suna kai hare-hare.
“Abin takaicin shi ne mutum 22 sun mutu a harin, daga ciki har da wasu masu aikin sa kai da suka yi ƙoƙarin kare kansu,” kamar yadda wani jami’i ya tabbatar.
Wani mazaunin kusa da lamarin ya faru ne ya tabbatar da adadin mutanen da aka kashe.
Hari da yammaci
Jami’in ya ce maharan sun kai harin ne a kan babura a ƙauyen da misalin ƙarfe huɗu na yamma.
“Sun soma harbi inda suka kashe mutane a wurin,” kamar yadda ya bayyana.
Nijar na fama da matsaloli biyu na masu tayar da ƙayar baya – wato rikicin da aka jima ana yi daga kudu maso gabashin ƙasar wanda ya fito daga Nijeriya da kuma wanda take fama da shi a yammacin ƙasar inda mayaƙa da ke tsallakawa daga Mali da Burkina Faso suke haddasawa.
Matsalar tsaro da ta ƙi cinyewa
A lokacin da shugabannin soji suka kifar da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban kasa Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulun 2023, sojojin sun ce sun yi juyin mulkin ne sakamakon taɓarɓarewar tsari a ƙasar.
A ranar 17 ga watan Disamba, wanda ya jagoranci juyin mulkin Janar Abdourahamane Tiani ya ce matsalar tsaron “na raguwa a hankali” bayan sojojin sun samu nasara sosai a yaƙin da suke yi.