Bayan ruwan sama mai karfi da aka zabga a ranar Juma’a, an samu ambaliyar ruwa a wasu sassa na Accra babban birnin Ghana.
Ruwan saman mai karfi wanda aka yi shi na mintoci, ya yi ambaliya inda ya mamaye hanyoyin mota.
Daga cikin hanoyiyin har da hanyar Accra zuwa Tema da kuma hanyar Shiashie zuwa Madina, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar Ghana ta ruwaito.
Bidiyoyin da aka rinka yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwan ya yi barna inda har ya kusan shanye motocin da ke bisa titi.
Wani bidiyon da aka wallafa a shafin X ya nuna yadda ruwan saman ya yi matukar barna a unguwar Ashaiman inda har ruwan ya shiga babban kantin nan na China Mall.
Wannan ambaliyar na zuwa ne kwanaki biyu bayan daruruwan mutane sun rasa muhallansu sakamakon igiyar ruwa wadda ta jawo ambaliya garuruwan Keta da Anloga wadanda ke gabar teku a yankin Volta na Ghana.
Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito yadda mazauna garuruwan suka koka kan yadda ruwan ya lalata musu gidaje da kuma amfanin gona.
Wani manomi ya shaida cewa duka amfanin gonarsa wadanda suka hada da tumatir da kubewa da barkono duk sun lalace.
A bana ambaliyar ruwa ta yi sanadin asarar dumbin rayuka da dukiyoyi a fadin duniya.
Ko a cikin ‘yan kwanakin nan sai da ambaliyar ta yi sanadin mutuwar dubban mutane a kasar Libiya da asarar dukiyoyi.