Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya jawo ambaliyar ruwa a sassan Somalia ya sa mutum fiye da rabin miliyan sun tsere daga gidajensu sannan akalla mutum 30 sun mutu, a cewar Ministan Watsa Labarai na kasar.
Daud Aweis ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar Lahadi.
Tun farkon watan da muke ciki ake shatata ruwan sama a kasar ta Somalia sakamakon sauyin yanayi na El Nino da ke faruwa saboda dumamar ruwa, abin da ya janyo rushewar gidaje sannan ruwa ya shanye gonaki.
Wannan bala'i na faruwa ne a yayin da kasar ke ci gaba da fama da fari wanda ya jefa miliyoyin 'yan kasar Somali fuskantar hatsarin kamuwa da tamowa.
"Mutum rabin miliyan sun tsere daga gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa," in ji Ministan Watsa Labarai Daud Aweis, inda ya yi gargadin cewa lamarin yana iya shafar mutum sama da miliyan daya da dubu dari biyu.
Ya kara da cewa jami'an gwamnati sun tabbatar da mutuwar mutum 31 ko da yake ya kara da cewa "akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu zai karu".
Ambaliyar ruwan ta fi yin barna a lardin Gedo da ke kudancin Somalia da lardin Hiran na tsakiya inda Kogin Shabelle ya balle, hanyoyi suka lalace sannan ta rusa gidaje a garin Beledweyne.
Kusan mutum 200,000 ne suka rabu da gidajensu a Beledweyne lokacin da kogin ya balle a watan Mayu.
Somalia na daya daga cikin kasashen da suka fi fama da illolin sauyin yanayi kuma ba ta da isassun kayan shawo kan irin wannan matsala.
A makon jiya, Hukumar Bayar da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ta ce kasar tana fuskantar "ambaliyar ruwa irin ta mafi muni a tarihi" sannan ta yi gargadin cewa tana iya shafar kusan mutum miliyan 1.6.