Al’ummar wata unguwa Briqueterie da ke yankin Yaounde 2 a Jamhuriyar Kamaru sun koka kan yadda suke fama da azabar annobar kuɗin-cizo tun ranar 6 ga watan Disamban nan.
“Kwana ake suna cizon yara inda suke kasa barci saboda azabar ƙaiƙayi da susa, duk jikinsu tabon cizo ne. Da farko na zaci sauro ne, sai da na zo ina gyara gado sai kawai na ga kuɗin-cizo duk sun baibaye gadon,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kamaru ya rawaito wata mata Aminatou Lamy na fada.
Mazauna yankin da dama sun ce “idan muka kashe su sai mu ga jini da yawa kuma sai su yi ta wari.
"Da zarar ka shiga gidan da suke fama da kuɗin-cizo to fa ko ɗaya ne ya maƙale maka ka je gida da shi to nan da nan za su fara hayayyafa, ga su da shan jini.”
Ministan Harkar Lafiya na Kamaru ya bayar da shawarwari na yadda ya kamata mutane su ɗauki matakan kariya don kashe kuɗin-cizo da hana ci gaba da yaɗuwarsu.
Daga cikin matakan da ya faɗa akwai; yawan goge kayan katako da ke gida da rage cunkuson kaya da tabbatar da kuma tsaftace ɗakuna da kowane lungu da saƙo.
Kazalika rage yawan kaya a cikin durowowi da wanke kaya a cikin ruwan zafi zai taimaka wajen kashe kuɗin-cizo in ji ministan. Sannan a tabbatar an zazzage kaya da tsara su sosai kafin shigar dasu cikin gida bayan dawowa daga tafiya.
Jami’an ma’aikatar lafiyar sun ce mutane su kwantar da hankulansu, ta yadda za su iya mayar da hankali wajen bin matakan rage yaɗuwar ƙwarin.
Labari mai alaƙa: Kudin-cizo: Abu shida game da kwaron da ya addabi Faransa
Sannan sun ja kunnen mutane don yin taka tsantsan wajen amfani da magunguna ƙwari barkatai don gudun ka da su yi amfani da masu illa da cutarwa.
A watan Oktoban da ya gabata ma annobar kuɗin-cizo ta shiga ƙasar Faransa inda ta addabi mutane, lmarin da ya jawo dakatar da al’amura da dama ciki har da rufe makarantu.
Kudin-cizo wani kwaro ne mai siffar kwai, wanda hanyar samun abincinsa ita ce shan jini zalla na bil adama ko dabbobi a lokacin da suke bacci.
Kudin-cizo launinsa ja ne da ruwan kasa, ba shi da fiffike, kuma yana da tsawon mita daya zuwa bakwai. Wannan kwaron zai iya rayuwa tsawon watanni bakwai ba tare da ya sha jini.