Guduwar likitoci ya shafi kasashen Afirka da dama. Photo: Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Ya zuwa yanzu matakin da Nijeriya ta dauka na farfado da ayyukan kiwon lafiya a kasar ta hanyar kokarin hana su guduwa tare da dawo da kwararrun likitoci zuwa kasar ya samar da sakamako mai kyau.

Dr. Kamar Adeleke, kwararren likitan zuciya ne da ya bar aikinsa mai tsoka a Amurka tare da koma wa kasarsa Nijeriya, na daga cikin 'yan kalilan na likitocin da suka amsa abun da ya ambata da kiran tunaninsa.

Ya fada wa TRT Afirka cewa "idan ban dawo Nijeriya ba na yi zama na a wancan bangaren, Ubangiji zai tambaye ni ya aka yi na ki taimakon kasa ta a lokacin da na ke da iko."

Dr. Adeleke ya tuno da yadda ya dinga jin ya kamata ya koma Nijeriya bayan ya je wani aikin duba lafiya na wucin gadi inda ya fahimci ciwon zuciya na daga cututtukan da ke kashe yan kasar..

Ba shi kadai ne likitan da ya koma Nijeriya ba, kasar da aka binne cibiyarsa.

Kasashen Afirka na fama da cututtuka amma duk da haka likitoci na guduwa. Photo: Reuters

Akwai wasu likitocin irin su Adeleke da suka dauki wannan mataki na koma wa gida, duk da wahalar yin hakan inda suka hakura da dumbin kudaden da suke samu a kasashen waje.

Labaran wadanda ke komawa na ci gaba da zama abun muhawara game da yadda ma'aikatan lafiya ke guduwa daga kasar da ta fi yawan jama'a a Afirka.

Cutar da mutane

Hijirar ma'aikatan lafiya daga Afirka ko sauran kasashe masu tasowa ba sabon abu ba ne.

Amma kasashe da dama a nahiyar na kara damuwa game da wannan al'ada da ke ci gaba..

Daga Ghana da ke Yammacin Afirka zuwa Zimbabwe a kudancin nahiyar, da Kenya da ke Gabashin Afirka mahukunta na ta fafutukar nemo hanyoyin da za su magance guduwar kwararrun likitoci daga kasashen.

Mataimakin Shugaban Kasar Zimbabwe Chiwenga na da ra'ayin a dinga hukunta masu dauke kwararru zuwa wasu kasashen. Photo: Reuters

A watan Afrilu, kafafan yada labarai sun ruwaito Mataimakin Shugaban kasar Zimbabwe Costantino Chiwenga na cewa kasar na shirin mayar da daukar likitocinsu da wasu kasashe ke yi babban laifi..

Chiwenga wanda shi ne Ministan Lafiya na Zimbabwe ya ce irin wannan daukar aiki - musamman ma daga kasashen Yamma - abu ne da ke cutar da kasarsa da ta fukanci guduwar ma'aikatan lafiya a 'yan shekarun nan.

An rawaito Chiwenga na cewa "Idan wani da gangan ya dauki ma'aikata don jefa kasa a wahala, wannan laifi ne na bil'adama. Mutane na mutuwa a asibitoci saboda babu ma'aikatan jinya da likitoci. Dole ne a dauki wannan da muhimmanci."

Kwanaki a Nijeriya, wani kamfani a Abuja babban birnin kasar ya sanar da farautar ma'aikatan lafiya da za su yi aiki a Ingila.

Yadda aka ga likitoci na bin layi don tattaunawa kan wannan aiki,a bu ne kamar a mafarki, a lokacin da kasar ta Yammacin Afirka ke kokarin magance abun da ake kira japa, ko guduwa don neman kudi a kasar waje.

Dawo gida

Duk da cewa daga baya Ingila ta dakatar da daukar ma'aikatan lafiya daga kasashe masu tasowa irin su Nijeriya, babu alamun tsayawar guduwar likitocin.

Tuni aka gabatar da kudirin dokar hana likitoci barin Nijeriya a gaban majalisar dokokin kasar.

Dr Adeleke kwararren likita ne da ya kasu a Amurka kafin ya dawo Nijeriya. Photo: Adeleke

A lokacin da ake ta zance da yada labarin likitocin da ke barin Nijeriya, wasu kuma na koma wa kasar don taka rawa a sashen kula da lafiya, inda suke cewa kudin da ake samu a kasashen waje ba kamar yadda ake hangen su daga nesa ba.

Haka kuma suna korafi game da rashin kayan aiki a gida, Rashin isassun kayan aiki na iya zama daya daga cikin dalilan da suka sanya manyan 'yan siyasa a kasar ke fita kasashen waje neman lafiya.

Wasu daga cikin likitocin da suke dawo wa gida don bayar da gudunmowa ta hanyar horar da matasa masu tasowa a cikin likitoci da kuma amfani d akwarwar da suka samu a kasashen waje.

Babu gajeriyar hanya

Dr Abubakar Sa'idu wanda a yanzu haka yake aiki a a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe a arewa maso-gabashin Nijeriya, na daya daga cikin likitocin da suka dawo gida.

Rashin ingantattun kayan aiki na daga kalubalen da harkar kula da lafiya ke fuskanta a kasashen Afirka da suka hada da Ghana, Photo: Reuters

Dr Sa'idu ya yi aiki a Asibirin Koyarwa na Jami'ar King Khalid da ke Riyadh, Saudiyya na tsawon shekara biyar kafin ya koma Nijeriya don samun damar tarbiyyar yaransa a gida, sannan ya zauna tare da iyayensa.

"Eh, aikin na da wahala sosai. amma kana da kayan aiki mafiya kyau; saboda haka yana da dadi." in ji shi a yayin tattaunawa da TRT Afrika kan yanayin aiki da ya tsinci kansa a ciki a Saudiyya.

Ya kara da cewa "Kana aiki ne a waje mafi kyau da inganci kuma kana dukkan kayan gudanar da bincike. Albashi na da tsoka kuma muhallin zama na da kyau sosai."

A karshen shekarar da ta gabata, shugaban Kungiyar Likitoci, Uche Rowland ya ce, sama da likitocin Nijeriya 5,600 ne suka yi hijira zuwa Ingila a shekaru takwas din da suka gabata.

Kasancewar ya yi aiki a Nijeriya da kasar waje, Dr Sa'idu na da ra'ayin babu wata gajeriyar hanya ta rufe gibin da likitocin da ke barin Nijeriya suka samar.

Afirka na da mutane matasa mafi yawa a duniya tare da yawan ma'aikata. Photo: Reuters

Kungiyar ta bayyana Nijeriya na da likitoci 24,000 da ke aiki a cikin kasar, kuma ana bukatar 360,000 don cimma adadin da WHO ta bayyana ana bukata.

"Babu wani zabi da ya wuce samar da likitoci da yawa", in ji Dr. Saidu inda ya kara da cewa "Muna aikin kara yawan kwalejojin lafiya da Asibitocin Koyarwa da fara Manyan karatun Digiri."

Amma duba da lokacin da hakan ke dauka wajen horar da likitoci da kuma yadda da yawa daga sabbin likitocin na son barin kasar, akwai bukatar sake duba yadda ake guduwa daga Nijeriya.

Koyon darasi

Dr Adeleke na da yakinin cewa za a iya cimma wannan buri ta hanyar samar da kyakkyawan yanayi da kayan aiki, wuta, tsaro da kyautatawa ma'aikata.

Ya ce kasar za ta iya koyon yadda indiya ta janyo hankalin likitocinta da dama suka koma gida daga kasashen waje ta hanyar ba su kudade a yawa da samar da kayan aiki.

A lokacin annobar Covid-19, kasashe sun sha fama da karancin likitoci. Photo: Reuters

A nasa bangaren, Dr Sa'du na tunanin tare da samun ingantattun kayan aiki, asibitocin Nijeriya za su gyaru.

"Abu mafi muhimmanci shi ne a inganta yanayin kula da lafiya a asibitoci tare da zuba kayan da ake bukata.

"Sannan a samar da kudade don gudanar da bincike, kyautata yanayin aiki da muhalli mai tsaro,” Dr Sa'idu ya bayar da shawara.

A tare da hakan, wadanda suka dawo gida na ci gaba da bayar da gudunmowarsu a bangaren kula da lafiya.

Dr Adeleke ya yi nuni da cewa saboda kokarin da tsarin kula da lafiya na bangare uku ya samar, kwalejin Likitoci ta Yammacin Afirka na kokarin kawo shirinta na aikin zuciya ba tare da yanka kirji ba zuwa Nijeriya daga Ghana.

Batun 'yan Nijeriya za su samu kyakkyawan yanayin kula da lafiya lamba daya ba abu ne da ba zai yiwu ba, mafarki ne da zai iya zama gaske a nan kusa.

TRT Afrika