Hukomomi a Jamhuriyar Nijar sun kona tarin kwayoyi nau'i daban-daban da aka yi nasarar kamawa a hannun masu sha da safarar miyagun kwayoyin.
An yi gangamin taron kona kwayoyin ne albarkacin ranar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi da ake yi duk ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara.
An gudanar da wannan aiki ne a karkashin jagorancin Ministan Harkokin Cikin Gida na Jamhuriyar ta Nijar, Malam Hamadou Souley Adamou.
An kiyasta kudin kwayar da aka kona da cewa ya haura CFA biliyan 26.
Kasar Nijar da ke yankin Afirka ta Yamma na daya daga cikin kasashen da dillalan kwayar ke amfani da ita wajen tsallakawa zuwa kasashen Larabawa irin su Libiya da Aljeriya ko kuma zuwa kasashen Turai.
TRT Afrika