Hukumomin Afirka ta Kudu sun ce ana cigaba da neman ɗan wasan ƙwallon zari-ruga na Faransa Medhi Narjissi da ya ɓace a birnin Cape Town.
Kafar yada labarai na gwamnati ƙasar SABC, ta rawaito cewa wata guguwa ce daga cikin teku ta tafi da Narjissi yayin da yake iyo tare da wasu abokan wasansa a bakin Tekun Diaz na Cape Point kimanin mako guda da ya wuce.
Ɗan wasan na ɗaya daga cikin tawagar 'yan wasan Faransa 'yan kasa da shekara 18 da za su buga gasar ƙwallon zari-ruga a Afirka ta Kudu tare da tawagar ƙasashe masu masauƙin baki wato Ingila da Ireland da kuma Georgia.
Daga baya ne aka cire Faransa daga gasar ta U18 ta kasa da kasa.
'Mawuyacin yanayi'
Mai magana da yawun Cibiyar Ceto a Teku ta Kasa, Craig Lambinon, ya ce Ma’aikatan Lafiya na aikin Gaggawa da hukumar ta aika suna nan a shirye don taimakawa 'yan sanda a ci gaba da binciƙen da suke yi.
''Alhininmu yana tare da ɗangi da abokai da kuma tawagar 'yan wasan ƙwallon zari-ruga bisa ga batar matashin a wannan mawuyacin yanayi.
Hukumomin Faransa da hukumomin yawon yawon buɗe ido na birnin Cape Town suna taimakawa da shawarwari da kuma kayan aiki," in ji Lambinon
Ƙungiyar wasan ƙwallon zari-zuga ta SA Rugby ta ce za ta tallafa wa tawagar Narjissi ta Faransa.
An tura jirage marasa matuƙi da masu saukar ungulu don taimakawa a aikin binciken da ake yi.