Ce-ce-ku-ce ya mamaye taron COP28 na sauyin yanayi da ake yi a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa yayin da ‘yan Nijeriya ke korafi kan dimbin ‘yan kasar da suka halarci taron.
Hadaddiyar Daular Larabawa tana da mahalarta mafi yawa -- wato mutum 4,409, Brazil na da mahalarta 3,081 sai Nijeriya da China da kowaccensu ke da mahalarta 1,411.
Wannan dalili ne ya sa ‘yan Nijeriya da dama musamman a shafukan sada zumunta suka rika korafi cewa bai kamata gwamnatin kasarsu ta dauki nauyin dimbin mutane don halartar taron ba a daidai lokacin da kasar ke fama da matsaloli na matsin tattalin arziki.
Sai dai a sanarwar da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ba ita ta dauki nauyin mutum 1,411 da ke halartar taron ba, inda ta ce akwai mutane da dama da kamfanoni suka dauki nauyinsu daga kasar.
Korafin wasu ‘yan Nijeriya
Daga cikin masu yin wannan korafin, har da dan takarar shugabancin Nijeriya a Jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, wanda ya yi wa kasar shagube tare da caccakar gwamnati a kaikace kan wannan mataki.
Ita ma sanarwar da mai magana da yawun Jam’iyyar PDP Debo Ologunagba ya fitar ta yi Allah wadai da wannan lamari inda ta ce asarar kudin kasa ne.
Jam’iyyar ta ce bai kamata gwamnatin Nijeriya ta kashe irin wadannan kudaden ba a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki.
Me gwamnatin Nijeriya ke cewa?
A wata sanarwa da Ma’aikatar Watsa Labarai ta Nijeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta tabbatar da cewa akwai ‘yan kasar da dama da ba gwamnatin Nijeriya ce ta dauki nauyinsu ba.
Gwamnatin Nijeriya ta ce daga cikin wadanda suka halarci taron daga kasar akwai shugaban bankin UBA Tony Elumelu da Abdul Samad Rabiu Shugaban BUA da sauran ‘yan kasuwa.
Gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa wadannan ‘yan kasuwar sun taho da ma’aikatansu domin ci-gaban kasuwancinsu, kuma suna daga cikin mutum 1,411 daga Nijeriya inda ta ce ba gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyinsu ba.
Daya daga cikin hadiman tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari wato Bashir Ahmed ya tabbatar da batun na gwamnatin Nijeriyar inda ya wallafa takardar gayyatar da aka yi masa tare da cewa shi ya dauki nauyin kansa.