Daga Abdulwasiu Hassan
Korar da gwamnatin Chadi ta yi wa jakadan Jamus daga kasarta, Jan Christian Gordon Kricke, a baya-bayan nan kan “rashin ladabi,” ya kara fito da halin rashin tsoro da kasashen Afrirka ke nunawa a huldarsu da kasashen Yammacin duniya da Amurka.
An umarci jakadan da ya bar kasar ne bayan ya yi suka kan jinkirin da aka samu wajen shirya zabe tun bayan da wata kotu ta yanke hukuncin cewar shugaban mulkin soji, Mahamat Idriss Deby, zai iya tsayawa takara a zaben 2024, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito majiyoyin gwamnati na cewa.
Ita ma kasar Jamus ta dau fansa ta hanyar korar jakadiyar Chadi, Mariam Ali Moussa daga kasarta.
Wannan ya faru ne watanni bayan gwamnatin kasar Mali ta kori jakadan Faransa kan zargin sa da “miyagun kalaman gaba” da Ministan Harkokin Turai da na Ketare na Faransan, Jean-Yves Le Drian ya yi a kan Malin.
An bukaci jakadan ya bar kasar a lokacin da Rasha ke kara tasiri a kasar, kuma daidai lokacin da kasashen Yammacin duniya ke cewa an tura sojojin haya na Rasha da ke aiki da kamfanin Wagner zuwa Mali.
Bayan an kori jakadan Faransa a kasar, ‘yan Mali sun bazama kan titunan babban birnin kasar Bamako, don nuna farin cikin korar, suna kada tutar Rasha tare da kona mutum-mutumin shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Kusan a wannan lokacin ne ita ma gwamnatin sojin Burkina Faso ta nemi cire jakadan Faransa daga kasar.
Ta kuma nemi dakarun Faransa da ke yakar kungiyar ISIS da Al Qaeda su bar kasar, bayan ‘yan kasar sun yi zanga-zangar nuna kin kasancewar sojojin Faransa a kasarsu.
A bara ma kasar Mali mai makwabtaka ta nemi dakarun Faransa da su fice mata daga kasarta.
A nata bangaren, a kusan karshen shekarar da ta gabata, ita ma Nijeriya ta bai wa ‘yan kasarta masu ziyara a Amurka da Birtaniya da su yi hankali da fasfo da kudadensu da sauran abubuwa masu kima don ka da sace su a kasashen.
A lokacin da yake zanta wa da manema labarai a Abuja, Ministan Watsa Labaran Nijeriya Lai Mohammed ya ba da misali na irin wadanda hakan ta faru da su a Birtaniya.
“Akwai 'yan Nijeriya da dama da aka sace musu abubuwa masu daraja musamman a shagunan da ke Titin Oxford" .
Shawarin da gwamnatin Nijeriya ta bai wa ‘yan kasar sun zo ne wata daya bayan hukumomin Amurka da Birtaniya suka fitar da sanarwar kan hadari na yiyuwar kai harin ta’addanci a babban birnin kasar.
Me a yanzu shugabannin Afirka ke nuna kafiya a huldarsu da kasashen Yammacin duniya?
Masu sharhi suna ganin wannan sauyin na yadda shuwagabannin Afirka ke hulda da kasashen yammacin duniya masu karfi na da alaka da yadda huldar diflomasiyya ke sauyawa a duniya.
Wasu kuma na ganin har da yadda kasashen Yammacin duniya ke saka baki tare da yin tasiri kan harkokin kasashen Afirka fiye da yadda ya kamata.
"Wani abu da ake ganin yana kara jawo sauyin shi ne girman China a matsayinta ta kasar da ta fi zuba jari a kan ababen more rayuwa a Afirka, da kuma babbar barakar da aka samu tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya,” in ji Dr Jibrin Ibrahim, babban jami’i a cibiyar nazarin Cigaban Dimokradiyya da ke Abuja, Nijeriyaa.
Baya ga haka, "wani abu da ke kara fitowa karara shi ne yadda kasashen Afirka a yanzu suke ganin ikon iya cutar da su da kasashen Yammacin duniya ke da shi “ya ragu sosai,” in ji Dr Jibrin.
“Shugabannin Afrika na kara samun karfin gwiwa wajen tunkarar kasashen Yammacin duniya saboda muhimmin sauyin da aka samu a fagen diflomasiyya cikin ‘yan shekarun da suka gabata,” in ji shi.
“Wannan sabon yanayin a fagen diflomasiyya ya samar da zabi ga kasashen Afirka wadanda suka gani karara cewar za su iya takara da yammacin duniya kuma su tsira a fagen siysar duniya,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
“Wannan shi ya sa za ka iya gani a halin yanzu irin ikon da wasu kasashen yankin Sahel suke da shi na iya korar Faransa daga kasashensu, duk da cewa ita ta raine su, lamarin da a baya ba a taba zaton zai faru ba,” a cewarsa.
Me sabon salon ke nufi ga nahiyar Afirka?
Wannan lamari ne da ya zamto takobi mai baki biyu, in ji Farfesa Kamilu Sani Fagge na sashen koyar da Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kanon Nijeriya.
“Wannan zai taimaka musu (shugabannin Afirka) su dogara da kansu,” kamar yadda Farfesa Fagge ya shaida wa TRT Afrika, amma ya yi gargadi cewa idan har kasashen Yammacin duniyar suka kakaba wa irin kasashen Afirkan takunkumi, to lamarin ka iya wahalar da al’ummarsu.
Ya kara da cewar irin wannan kafiyar a wasu lokutan tana iya janyo juyin mulki ko rikicin da zai iya kai wa ga wargaza kasa idan aka kulla makirci daga kasashen waje.
A wani bangaren kuma, Dr Jibrin na tunanin cewa wannan wata dama ce mai kyau ga nahiyar.
“Ina ganin wannan wani yanayi ne na zabi mai kyau ga nahiyar Afirka. Wato Afirka za ta iya samun damar inganta yarjejeniya a bangarorin biyu masu karfi, kuma ta hakan za ta samu yajejeniyoyi da kuma yanayin da zai fi mata amfani bisa muradunta,” kamar yadda Dr Jibo ya shaida wa TRT.
Taka-tsan-tsan
Yayin da kasashen Afirka suka sha fama da juyin mulki da sauye-sauye na gaggawa wadanda aka shirya daga wajen nahiyar a baya, masu sharhi na ganin dole gwamnatocin su kasance masu kula da muradunsu da kuma yanayin da suke ciki a fagen diflomasiyyar da ke sauyawa.
Duk da cewar Farfesa Fagge ya yi amannar cewar ya kamata kasashen Afirka su dogara da kansu, ya ce “hakan ba ya nufin mu yi fito-na-fito.”
Ya ce kasashen Afirka za su iya samar da hulda mai amfani da kasashen Yammacin duniya ta hanyar kyautata diflomasiyya.
Dr Jibrin Ibrahim ma yana da wannan tunanin. “Ina ganin yana da muhimmanci a yi tunani da taka tsan-tsan kan yadda za a yi wadannan abubuwan,”kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
“Musamman shugabannin Afirka na bukatar su yi amfani da ilimi mai yawa da basira tare da bude zuciyoyinsu wajen gane yadda duniya take tafiya a halin yanzu, don su fahimci zabin da suke da shi, su tantance haduran da ke akwai sai kuma su yanke shawara a kan fahimtar da ke a bayyane,” in ji shi.