Hukumar Leken Asiri ta Kasa ta Turkiyya (MIT) ta kama tare da dawo da wani babban jami'in Daesh da ake nema ruwa a jallo, in ji majiyoyin tsaron Turkiyya a ranar Litinin.
Ana zargin wanda aka kaman, wanda aka bayyana sunansa da Talip Guler, wanda aka fi sani da "Abdusselam Turki," yana aiki a cikin tsarin da ake kira "Jihar Turkiyya" na Daesh, a cewar bayanan da majiyoyin tsaro suka fitar.
MIT ta ce aikin leken asirin ya gano Guler a matsayin dan'uwan Kasim Guler, wanda a baya ya yi aiki a matsayin shugaban Daesh kuma jami'in kudi kafin a kama shi a wani farmaki a 2021 tare da kawo shi Turkiyya.
Ayyukan leƙen asiri sun bi sahun Daesh
A cewar majiyoyin tsaro, MIT ta gano cewa Talip Guler ya shiga Syria ba bisa ƙa'ida ba a watan Janairun 2014, daga baya kuma ya yi aiki tare da manyan jagororin Daesh, ciki har da ɗan'uwansa.
Hukumar leƙen asiri ta ce ta ci gaba da sa ido kan ayyukan Guler bayan kama Kasim Guler, kuma daga ƙarshe ta tabbatar da an mayar da shi daga yankunan rikici zuwa Turkiyya.
Hukumomi sun ce wannan farmaki wani ɓangare ne na babban ƙoƙari na wargaza hanyoyin sadarwa na Daesh, hana kai hare-haren da aka shirya kai wa da kuma bankado da dakile tsarin ɗaukar ma'aikata na ƙungiyoyi da ke da alaƙa da ƙungiyar.
Wanda ake zargin ya bayar da bayanai game da ayyukan Daesh
A lokacin da ake yi masa tambayoyi, an rawaito Talip Guler ya bayar da bayanai game da tsarin koyar da tsattsauran ra'ayin kungiyar a Turkiyya, shigar sa Syria ba bisa ka'ida ba, daukar sa aiki a Daesh da ayyukan da ya gudanar a cikin kungiyar.
Majiyoyin tsaro sun ce shaidarsa ta ƙunshi bayanai game da ayyukan da aka gudanar tare da Kasim Guler, wanda a baya ya rike babban mukami a reshen Daesh na Turkiyya.
MIT ta ce ayyukan leken asiri da ake ci gaba da yi na ci gaba da nufar bangarorin Daesh da kuma hana kungiyar sake gina hanyoyin sadarwa ko shirya hare-hare kan Turkiyya.





















