| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Fitacciyar mawaƙiyar Afirka Ta Kudu ta soke kalankuwarta a Legas bayan an kori baƙi daga ƙasarta
'Yan Nijeriya a kafafan watsa labarai sun nemi a ƙaurace wa kalankuwar bisa zanga-zanga ƙin jinin 'yan ci-rani da aka yi ta yi a Afirka Ta Kudu.
Fitacciyar mawaƙiyar Afirka Ta Kudu ta soke kalankuwarta a Legas bayan an kori baƙi daga ƙasarta
TSOHON HOTO: Tyla ta halarci wani bikin ba da kyauta na mawaƙa mata na Billboard Women in Music Awards da aka yi a Los Angeles, California.


Fitacciyar mawaƙiyar Afirka ta Kudu mai rubuta waƙoƙi Tyla ta soke wata kalankuwarta da aka shirya yi a Nijeriya yayin da tashin hankali bisa ‘yan ci-rani ke tarnaƙi ga dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Ba a ba da dalili na sauya tafiyar waƙartan ba, amma matakin ya zo ne bayan wasu ‘yan Nijeriya a kafafan sada zumunta sun yi kira da a ƙaurace wa kalankuwarta.

An shafe watanni, inda Afirka Ta Kudu ta kasance wani wuri na nzaga-zanga - kan ‘yan ci-rani ‘yan Afirka waɗanda masu zanga-zanga suka ɗaura wa alhaƙin aikata laifuka da rashin ayyukan yi da kuma matsa wa ababen more rayuwa.

Nijeriya ta kasance mai magana sosai bisa lamarin kuma tashe-tashen hankula sun bayyana yayin da manyan jami’ai daga Abuja da Pretoria suka haɗu a wannan makon a ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya.

Tyla, wadda aka sani da fitattun waƙoƙi irin su "Water" da kuma waƙa tare da mawaƙan Amurka irin su Cardi B da Travis Scott, a ranar Litinin ta bayyana wuraren da za ta je ta yi waƙa a rangadin duniya da za ta yi na sabon faifen waƙar da ta yi mai suna, "A*POP", ciki har da Legas, babbn birnin tattalin arzikin Nijeriya, da New York da Paris da kuma Cape Town.

Zuwa safiyar Jumma’a, ɓangaren Legas na tafiyar waƙarta- wanda aka shirya ya yi daidai da lokacin waƙoƙi na Nijeriya da aka fi sani da suna "Detty December" - an cire shi daga jerin wuraren da za ta yi waƙa a adireshinta na intanet.

Wakilan Tyla ba su ba da amsa nan take ba ga buƙatar neman tsokaci kan batun.

Afirka Ta Kudu, Ɗaya daga cikin tattalin arziki da suka fi ƙarfin masa’antu a nahiyar, ya daɗe da kasancewa kuran ƙarfe ga ‘yan ci-rani da suke shigowa bisa ƙa’ida da waɗanda ke shigowa ba bisa ƙa’ida ba.

Amma ƙasar tana kuma fama da yawan rashin ayyukan yi da hidindimun more rayuwa masu rauni da, inda ake ɗaura wa ‘yan ci-rani alhakin da yawa daga cikin matsalolin kasar da kuma gazawar gwamnati, in ji masharhanta.

‘Yansandan Afirka Ta Kudu sun ce aƙalla baƙi huɗu ne aka kashe cikin hare-hare masu alaƙa da zanga-zangar ƙin jinin baƙi, duk da cewa wasu gwamnatocin Afirka da ke mayar da ‘yan ƙasashensu gida sun ba da rahoton adadin da ya fi haka.

Fiye da mutum 160,000 sun tsere daga ƙasar, kamar yadda wani adadin da kamfanin dillancin labaran AFP ya tara bisa alƙalluma daga gwamnatocin Afirka da ke mayar da ‘yan ƙasashensu gida cikin har da ‘yan Nijeriya 1,500.

Irin riƙon da Pretoria ta yi da lamarin ya sha suka yayin da ƙungiyoyin masu ƙin jinin suka danna cikin gidajen mutane kuma suke janye su zuwa cikin motocin ‘yansanda.