Yayin da aka buga wasanni 50 zuwa yanzu a gasar Kofin Duniya da ke gudana a Amurka, Canada, da Mexico, masu kallon wasannin sun lura da wani abu game da kyautar Gwarzon Wasa da ake bayarwa.
Saɓanin kyautar da aka bai wa gwarazan wasa irinsu Cristiano Ronaldo, Lionel Messi, Erling Haaland, Harry Kane, da Michael Olise, kyautar da aka bai wa ‘yanwasa Musulmi ta bambanta.
Duk bayan wasa, masoya da ke bibiyar wasan kan zaɓi ɗanwasan da ya fi nuna hazaƙa a wasan, ta hanyar jefa ƙuri’a ta intanet, sannan bayan kammala wasa, FIFA ta gabatar da kyauta ga ɗanwasan.
A gasar ta Kofin Duniya, kamfanin giya da yake “Michelob ULTRA” ne ya ɗauki nauyin kyautar. Don haka kyautar na ɗauke da tambarin kamfanin ɓaro-ɓaro lokacin da ake ɗaukar hoton ɗanwasa riƙe da ita.
Sai dai kasancewar kamfanin na giya ne, kuma akwai ‘yanwasa Musulmi da ke ƙyamar giya saboda haramcinta a Musulunci, ba a ganin tambarin kamfanin giyar a jikin kyautar da labulen bangon hotunan ‘yanwasan tare da kyautar.
Jawabi daga FIFA
Hakan aka gani a hotunan golan ;yanwasan da suka ci kyautar kamar Arda Guler na Turkiyya, da golan Qatar, Mahmoud Abunada, da ɗanwasan Canada, Ismael Kone, da Yan Diomande na Ivory Coast, da Ramin Rezaeian na Iran, da Emam Ashour na Masar, da Ismael Saibari na Maroko, Johan Manzambi na Switzerland, da sauransu.
Duka ‘yanwasan Musulmai ne, don haka da suka yi hoton kawai ya nuna rubutun 'Gwarzon Wasa' da kuma tambarin “FIFA World Cup”, ba tare da suna ko tambarin ”Michelob ULTRA” ba.
An ambato kakakin Hukumar FIFA na cewa, "AB InBev na gabatar da kyautar Gwarzon Wasa ga ɗanwasan da ya yi fice bayan kowane wasan Kofin Duniya na FIFA 2026, bayan masoya sun tantance.”
“Don girmama batun addini, an tanadi kyauta da labulen bango mara tambari idan ɗan wasan da aka zaɓa ya buƙata. Ana kuma amfani da wannan tsari ga ɗanwasan da bai kai shekarun iya shan giya ba a hukumance."














