Irin matsalar cikin gida da ta addabi jam’iyyun adawa na PDP da LP ta shiga sabuwar jam’iyyar haɗaka ta ADC inda hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta cire sunayen ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a ƙarƙashin Sanata David Mark daga shugabancin jam’iyyar da ke adireshinta na intanet.
Wannan zuwa ne yayin da jam’iyyar ta haɗaka ke samun ƙarin masu shigarta irin su tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso lamarin da ke yamutsa hazo a siyasar Nijeriya watanni tara gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Da yake bayyana wannan matakin na INEC a cikin wata sanarwa ranar Laraba, Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin watsa labarai da wayar da kan masu ƙada ƙuri’u, Mohammed Haruna, ya ce bayan cire sunayen David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaban ADC da babban sakataren ADC daga adireshinta na intanet, hukumar ba za ta amince da Nafiu Bala Gombe, wanda ke son kotu ta ayyana shi a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa ba.
Sanawar ta ce amicewa da wani daga cikin ɓangarorin biyu zai kasance yin katsalandan kan lamarin da ke gaban kotu.
INEC ta ce za ta dakatar da duk wata tuntuɓa da ɓangarorin biyu na jam’iyyar da ke rikici har zuwa lokacin da babbar kotun tarayya da ke Abuja za ta yanke hukunci kan batun.
Kazalika hukumar ta ce ba za ta sa ido kan ko wane babban taron jam’iyya da ɓangarorin biyu suka shirya ba.
INEC ta ce matakin nata ya biyo bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara game da Sanata David Mark da Nafiu Bala Gombe, tare da bayanai na shari’a masu karo da juna daga ɓangarorin biyu game da shugabancin jam’iyyar.
ADC ta yi watsi da matakin da INEC ta ɗauka, ta zargi APC
Jam’iyar ADC, a wata sanarwa da kakakinta Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu ta yi watsi da fahimtar hukumar INEC game da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke, tana mai zargin cewa hukumar ta ɗauki matakin ne bisa matsi daga gwamnati wadda ta ce tana jin tsoron karɓuwar da tafiyar jam’iyyar hamayyar ke samu duk da ƙoƙarinta na lalata dukkan jam’iyyun siyasa na hamayya da zummar ƙaƙaba mulkin jam’iyya ɗaya kan Nijeriya.
Jam’iyyar ta bayyana matsayar INEC a matsayin saɓa wa doka, tana mai nanata cewa za ta bayyana lamuran a fili, yayin da take gargaɗin cewa hukumar ta goyi bayan gwamnati maimakon ‘yan Nijeria.
ADC ta ce a halin yanzu tana nazari kan matakan da za ta iya ɗauka kuma nan ba da jimawa ba za ta bayyana matsayarta, tana mai kira ga ‘yan jam’iyyar da ma jama’ar ƙasar su ci gaba da jajircewa.
Asalin rikicin ADC
Rikicin shugabancin jam’iyyar ADC ya samo asali ne daga ajiye aikin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralph Okey Nwosu, da sauran mambobin gudanarwar jam’iyyar a watan Yulin shekarar 2025, lamarin da ya ba da dama ga naɗin sabon kwamitin gudanarwa ƙarƙashin shugabancin Sanata David Mark.
Sai dai kuma, Nafiu Bala Gombe, wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa a ƙarƙashin shugabancin Ralph Okey Nwosu, ya ƙalubalanci naɗin sabbin shugabannin jam’iyyar, yana mai cewa shi bai ajiye aiki ba. Saboda haka ya kamata a ce shi ne ya zama shugaban jam’iyyar bayan shugaban jam’iyyar ya ajiye aiki bisa tsarin mulkin jam’iyyar.
Wannan shi ya sa ya kai batun gaban wata babbar kotun Tarayya Nijeriya inda ya nemi ta hana INEC amincewa da shugabancin David Mark ta kuma bai wa hukumar zaɓen umarnin amincewa da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
Kawo yanzu dai jam’iyyar APC mai mulki ko kuma gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba su yi tsokaci game da zargin da jam’iyyar ta adawa ta yi ba.








