Belgium ta yanki tikitin zagaye na gaba na gasar Kofin Duniya a matakin ƙasashe 16, bayan nasarar da ta yi kan Senegal da ci 3-2 a safiyar Laraba.
Belgium ta ci ƙwallo biyu a makare, wanda ya tilasta kai wasan zuwa ƙarin lokaci kafin Youri Tielemans ya ci ƙwallo ta uku a minti na 125 ta bugun fenareti.
Tun da fari, Habib Diarra na Senegal ya zura ƙwallo ta farko a minti na 24, wanda ya ba Senegal fifiko a wasan na zagayen ‘yan-32.
A minti na 51 Ismail Sarr ya ci golan Belgium, Thibaut Courtois, wanda ya kai wasan ga 2-0.
Sai minti na 86 ne Romelu Lukaku na Belgium ya rama ƙwallo ɗaya, kafin kyaftin ɗinsu Tielemans ya zura ta biyu da ta mayar da wasan canjaras, sannan aka yi ƙarin lokaci.
A yanzu, sai ranar 6 ga Yuli ne Belgium za ta buga da Amurka don neman tsallakawa matakin kwatafainal.











