Bikin kamun kifi na Argungu: Kifin da ya kai kilogiram 59 ya ɗau hankalin dubban mutane
Mai kamun kifi daga Nijeriya Abubakar Usman ya lashe kyautar da aka ware wa gasar bayan kifin mai nauyin kilogiram 59 da ya samu. / Others
Bikin kamun kifi na Argungu: Kifin da ya kai kilogiram 59 ya ɗau hankalin dubban mutane
Hukumar UNESCO a Nijeriya ta sanya bikin kamun kifi na Argungu a matsayin ɗaya daga cikin manyan bukukuwan al'adu a Yammacin Afirka.
6 awanni baya

Kamun kifin da ya kai girma da nauyin kilogiram 59 shine babban abin da ya fi daukar hankali a bikin kamun kifi da al'adu na Argungu a Nijeriya, ɗaya daga cikin manyan bukukuwan al'adu a Yammacin Afirka.

An kawo karshen bikin karo na 61 da hukumar UNESCO ta sanya a cikin jerin manyan bukukuwan al’adu a Afirka da ake yi a jihar Kebbi da ke yankin arewa maso yammacin Nijeriya a ranar Asabar, 14 ga Fabrairu, bayan dakatarwar shekaru shida.

Fiye da masunta 50,000 daga ko'ina a faɗin Nijeriya da ƙasashe makwabtaka kamar Nijar, Kamaru da Chadi, da kuma Togo, me suka fafata a kogin Matan Fada suna neman babban rabo na kifin da ya fi ko wanne ƙato, yayin da ɗaruruwan mutane masu kallo suka hallara

Masutcin Nijeriya Abubakar Usman, wanda ya fito daga yankin Maiyama na jihar Kebbi ne ya lashe gasar bayan kama kifin da girma da kuma nauyinsa ya kai kilogiram 59.

Ya lashe kyautar sabbin motoci biyu da tsabar kuɗi na naira miliyan ɗaya, wanda yayi daidai da dala $739.

Ɗaruruwan ƙananan matsunta sun baza kayayyakin da suka samo a wata kasuwa ta wucin gadi da aka kafa a titunan da ke kusa.

Ƙarfafa yawon buɗe ido

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda shine babban baƙo na musamman a taron bikin, ya ce abin da ya gani "ya wuce iya bikin," ya ƙara da cewa taron shaida ne ga mutanen da yanzu ke "dawo da zaman lafiya."

Ya kuma yi nuni kan mahimmancin bikin wajen haɓaka al'adu, yawon buɗe ido, noma da kasuwanci.

Masu nishadantarwa sun ƙara launi da kyau ga taron, wanda ya mayar da garin Argungu wurin jan hankalin yawon buɗe ido na duniya.

Karo na ƙarshe kafin wannan na bikin shekara-shekara da aka gudanar a yi shi a shekarar 2020 kafin a dakatar da shi saboda annobar Covid-19 da ƙalubalen tsaro da ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane da kuma masu dauke da makamai suka haifar a yankin..

Ga Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mera, shirya bikin a wannan shekarar nasara ce ga zaman lafiya, al'adu da tarihi.

Tun daga shekarar 1934 aka fara shirya bikin kamun kifi da al'adu na Argungu ƙarkashin sarkin Argungu, Muhammad Sama, da nufin kawo karshen shekarun da aka kwashe na rashin yarda tsakanin al'ummarsa da kuma sarkin da ya fi karfi a yankin, Sultan na Sokoto a wancan lokacin, Hassan Dan-Mu'azu.

Tsawon shekaru da dama, bikin ya zama daya daga cikin manyan bukukuwan al'adu a Yammacin Afirka, inda ya jawo hankalin masu ziyara daga ƙasashen duniya kuma ya zama muhimmin darasi da ake koyarwa a makarantun Nijeriya.

A shekarar 2009, bikin ya samu matsayi a cikin jerin bukukuwan al’adu na hukumar UNESCO, wanda ya tilasta wa duniya baki daya ta kare shi daga duk wani akasi ko bacewa daga tarihi.