Tawagar Super Falcons ta mata ‘yanwasan ƙallon ƙafar Nijeriya ta doke takwararta ta Zambia da ci ɗaya mai ban haushi a wasansu na biyu na Rukunin C a Gasar Kofin Afirka ta Mata ta shekarar 2026 da ake yi a ƙasar Maroko.
Ƙwallon da Asisat Oshoala ta zura a ragar Zambia daga farkon wasan ne ya taimaka wa tawagar Nijeriyar mai ƙoƙarin kare kambinta wajen samun nasararta ta farko a gasar ta bana duk da cewa ta buga mafi yawan wasan ne da ‘yanwasan da ba su kai na Zambia ba.
Tawagar Falcons ta fito Filin Wasan Al Madina ranar Asabar ne da ƙalubalen kayen ban-mamaki da ta sha a hannun tawagar Malawi a wasanta na farko a gasar.
Golar tawagar, Chiamaka Nnadozie, wadda aka fi ɗaura wa laifin kayen, ta yi alƙawarin cewa sun koyi darrusa daga kuraran da suka yi a wancan wasan kuma sun shirya domin su sake farfaɗowa a wasan da ke biye da kayen.
Golar ta yi ta hawaye bayan nasarar, wani lamari da ke nuna yadda ta ji bayan an ƙarƙare wasan ba tare da ko ƙwallo ɗaya ya shiga ragarta ba .
Nijeriya ta doke Zambia da ci 5-0 a matakin kwata final na gasar WAFCON da ta wuce kuma tawagar ta nuna alamar iya maimata irin wannan a lokacin da ta fara zura ƙwallo a ragar Zambia minti takwas da fara wasa.
Oshoala, wadda ta dawo cikin masu fara wasa, ta yi gudu bayan wani ƙwallo da ata tura mata daga tsakiyar fili zuwa gidan Zambiaa, inda ta tsere wa ‘yan wasna baya biyu kafin ta sarrafa ƙwallon. Ƙwallon da ta fara bugawa ya tafi kai-tsaye ne ga Hazel Nali, amma ƙallon dawo ƙafar Oshoala inda ya koma cikin raga.
Sai dai kuma yanayin wasan ya sauya sosai minti 39 da fara wasa a lokacin da aka bai wa Oluwatosin Demehin jan kati bayan VAR ya sake duba ƙetar da ta yi wa ‘yarwasar Zambia Barbra Banda.
Wannan giɓin na adadin ya saka Nijeriya a ƙarƙashin matsi har zuwa ƙarshen wasan.
‘Yan Super Falcons sun nuna ƙarfin hali da kuma bin dabaru sau-da-ƙafa wajen kare ƙwallon da suka sha bayan adadinsu ya koma ‘yan wasa 10 kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Zambia ta kutsa tana neman ramawa bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Sai dai kuma, ƙoƙarin ‘yanwasan bayan Nijeriya da ma gagarumin ƙoƙarin kare gida na golar Nijeriya sun hana tawagar Copper Queens iya zura ƙwallo a ragar Nijeriya.
Wannan nasarar ta farfaɗo da fatan Falcons na kare kambinta.
Nijeriya za ta ƙarƙare wasanninta na matakin rukuni a wasan da za ta yi da Masar yayin da take neman shiga matakin sili ɗaya ƙwale na gasar kai tsaye.




















