Ƙarayrayi a kan Turkiyya da ɓata suna, ƙoƙarin Isra’ila ne na ɓoye “dabbancinta a Gaza”, kamar yadda shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan zaman majalisar ministoci a Ankara ranar Talata, Erdogan ya ce "ba ma mayar da hankali kan ƙarairayi da ɓata sunan da ake yi wa ƙasarmu daga mai kisan kai da ta zubar da jinin mutane 75,000 da basu ji ba basu gani ba a Gaza, yawancinsu ƙananan yara da mata."
Shugaban na Turkiyya ya bayyana zarge-zargen da ake yi wa Ankara a matsayin ƙoƙari karkatar da hankulan mutane da gangan, inda yake ishara ga tarihin Turkiyya na ba da mafaka ga waɗanda ke tsere wa cin-zarafi.
"Tarihinmu ya haɗa da kyawawan halaye na ba da mafaka ga waɗanda ke tsere wa cin-zarafi na Nazi," in ji Shugaba Erdogan.
"Waɗanda suke yi wa Turkiyya ɓatanci domin rufe dabbancinsu a Gaza sun fi kowa sanin hakan."
Shugaban na Turkiyyan ya kuma yi bayani game da ayyukan fasaha na Turkiyya masu muhimmanci, yana mai cewa bunƙasa ƙwarewa ta tauraron ɗan’adam ta wuce matakin zaɓi ga ƙasar.
"Ga Turkiyya, bunƙasa fasahar tauraron ɗan-Adam abu ne da ya zama wajibi, ba zaɓi ba ne," a cewar Erdogan .
Shugaba Erdogan ya bayyana goyon bayan Turkiyya ga Venezuela biyo bayan girgizar ƙasa biyu da suka afka wa ƙasar, yana mai ɗaukar alƙawarin tallafa wa mutanen Venezuela "da dukkan ƙarfinmu".
"Muna miƙa tallafinmu ga mutanen ƙasa da muka abokantaka da ‘yan’uwantaka Venezuela da dukkan ƙarfinmu," a cewar Erdogan.
Shugaban Turkiyyan ya ce Turkiyya ta tura jiragen soji biyu ɗauke da tawagogi na bincike da ceto tare da agajin jinƙai zuwa ƙasar Venezuela da girgizar ƙasa ta afkawa, kuma tawagogin sun riga sun fara ayyuka a ƙasar, inda suke aiki bisa tsare-tsaren ceto na ƙasa da ƙasa.
“Ƙananan hukumomin Turkiyya sun ƙaddamar da gangamin neman taimako domin agaza wa Venezuela,” in ji shi.
















