Wani babban jami’in Iran ya yi kira ga ’yan ƙasar da su rage amfani da man fetur a ranar Talata, yayin da ƙasar ke fuskantar matsalar shigo da isasshen mai saboda takunkumin sojin ruwan Amurka.
Kakakin Majalisar Dokokin Iran kuma babban mai shiga tattaunawar diflomasiyya, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce wani ɓangare na yawan amfani da man fetur ya samo asali ne daga masana’antu, ba daga ’yan ƙasa kaɗai ba.
Sai dai ya ce duk da haka, abin da ya fi muhimmanci shi ne rage yawan man da ake amfani da shi.
Washington ta kakaba takunkumin sojin ruwa ga tashoshin jiragen ruwan Iran ne bayan Tehran ta rufe Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar mai da iskar gas daga yankin Gulf.
Amurka ta kuma sanar da wasu sabbin takunkumai masu yawa da nufin ƙara matsa wa tattalin arzikin Iran lamba.
A kwanakin baya, an ga dogayen layukan motoci a gidajen mai da ke Tehran.
Mataimakin Shugaban Iran, Mohammad Jafar Ghaempanah, ya ce a makon da ya gabata man fetur din da ake samarwa a cikin gida bai wadatar ba, kuma saboda takunkumin sojin ruwan Amurka, Iran ba ta iya shigo da isasshen mai daga waje.
A baya-bayan nan, Fadar Shugaban Ƙasar ta ce za a sake duba adadin man fetur da ake ware wa ’yan ƙasa.
Ghalibaf ya ce rage amfani da man fetur na buƙatar haɗin kan jama’a, yana mai cewa idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata, Iran za ta iya dogaro da adadin man da take samarwa a cikin gida.
Ƙarin tallafin abinci
Yayin da hauhawar farashin kayayyaki da yaƙin ke ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga ’yan Iran, Ghalibaf ya kuma sanar da shirin ƙara tallafin gwamnati.
Ya ce gwamnati da majalisa sun ƙuduri aniyar ƙara kuɗin da ake warewa shirin tallafin abinci na lantarki, musamman ga iyalan da matsin tattalin arziki ya fi shafa.
A watan Disamban da ya gabata, zanga-zangar nuna damuwa kan matsalar tattalin arziki ta rikide zuwa babbar zanga-zangar adawa da gwamnati, wadda ta kai kololuwa a watan Janairu kafin jami’an tsaro su dakile ta.
Ghalibaf ya jaddada cewa jin daɗin jama’a na daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci ga gwamnati.
Ya ce, a matsayinsu na jami’an gwamnati, ya kamata duk ƙoƙarinsu ya mayar da hankali wajen rage wa jama’a matsin rayuwa da kuma rashin gamsuwa, domin jin daɗin jama’a muhimmin ginshiƙi ne ga gwamnati.























