An tilasta wa fiye da mutum 5,000 gudun hijira daga ƙauyuka 10 a jihar Darfur ta Yamma ta Sudan cikin ƙaruwar rashin tsaro da kuma arangama tsakanin sojoji da mayaƙan RSF, kamar yadda Hukumar da ke Kula da ‘Yancirani ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM), ta bayyana.
Hukumar ta MDD, a wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, ta ce tsarinta na bibiyar mutane ya yi kiyasin cewa mutum 5,135 sun tsere daga ƙauyukan Sirba na jihar Darfur ta Yamma zuwa ranar 8 ga watan Agusta biyo bayan ɓarkewar yaƙi a yankin Bir Saliba.
Da yawa daga cikin iyaen da lamarin ya shafa an tilasta musu barin muhallansu ne zuwa cikin Chadi, in ji hukumar.
A ranar Asabar, Gwamnan Darfur Minni Arko Minnawi ya ce sojin Sudan sun daƙile wani gagarumin harin da mayaƙan RSF suka ƙaddamar a kan Bir Saliba.
Muhimmin birni
Bir Saliba na arewa da El Geneina, baban birnin Darfur ta Yamma, kuma ana ganin wuri ne mai muhimmanci, saboda inda ya ke a kan hanyoyin da ke zuwa birnin. Yankin ya fuskanci yaƙi a-kai-a-kai tsakanin RSF da soji da dakarun da ke mara wa sojojin baya.
Yaƙi tsakanin sojin Sudan da RSF ya ci gaba tun ranar 15 ga watan Afrilu na shekarar 2023, biyo bayan rashin cim ma matsaya game da shigar da RSF ɗin cikin sojin ƙasar. Rikicin ya yi ajalin gomman dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da gidajensu.
Zuwa ƙarshen watan Yunin shekarar 2026, hukumar IOM ta tattara bayanan kimanin mutum miliyan 8.69 da aka raba da muhallansu a Sudan, tare da da mutum fiye da miliyan 4.64, waɗanda suka koma wasu yankuna a cikin ƙasar ko kuma suka ƙetara zuwa ƙasashe waje.






















