Ƙasar Chadi ta sanar a ranar Litinin cewa tana shirin janyewa daga Kotun Hukunta Laifuka ta Duniya (ICC), inda ta ce aikin kotun "yana da iyaka, kuma ba ya gudana bisa daidaito," sannan ya fi mayar da hankali a kan Afirka.
Wannan mataki ya biyo bayan na ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar, waɗanda a watan Satumba suka sanar da cewa za su janye daga ICC, kotun da ke shari'anta mutane kan laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama.
Shawarar da Chadi ta yanke ta biyo bayan "nazari mai zurfi kan ayyukan Kotun Hukunta Laifuka ta Duniya tun da ta fara aiki a shekarar 2002, da kuma nazarin nasarorinta waɗanda har yanzu aikinsu ke da iyaka da rashin daidaito," in ji mai magana da yawun gwamnatin ta Chadi a wata sanarwa.
Sannan ta yi Allah wadai da abin da ta kira mayar da hankalin ayyukan kotun a ƙasashen Afirka kaɗai. Daga cikin bincike 13 da kotun ta gudanar tun lokacin da ta fara aiki, guda tara sun shafi ƙasashen Afirka ne, yayin da huɗu kacal aka gudanar da su a sauran yankunan duniya "amma ba tare da samun wani ci-gaba na a-zo-a-gani ba," kamar yadda gwamnatin Chadi ta bayyana.
"Kotun ta tsare mutane bakwai ne kawai, kuma guda shida daga cikinsu ana shari'arsu ne kan abubuwan da suka shafi Afirka," in ji sanarwar.

A cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na ministan ma’aikatar harkokin waje a makon da ya gabata, shawarar ta janyewa daga ICC ta biyo bayan wata buƙata ce daga Amurka. Sanarwar ta ce mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da al'amuran Afirka ya matsa wa gwamnatin Chadi lamba don ta sake duban zamanta mamba a ICC yayin wani kiran waya da aka yi a ranar Alhamis.
"Ɓangaren Amurka ya nuna damuwarsa kan yadda wannan cibiya ke aiki sannan ya bukaci Chadi da ta sake duba zamanta mamba bisa Yarjejeniyar Rome," in ji sanarwar.
Burkina Faso, Mali da Nijar — duka ƙasashe ne na yankin Sahel a Yammacin Afirka da gwamnatocin soji ke mulkinsu — sun kira kotun a matsayin "wata hanyar danniya ta sabon tsarin mulkin mallaka a hannun masu tsarin mamaya na duniya."












