Kusan rabin Musulman da ke rayuwa a Turai na fuskantar nuna wariyar launin fata da bambanci a rayuwarsu ta yau da kullum, in ji Hukumar Tarayyar Turai Kan Manyan Hakkokin Dan Adam a wani rahoto da ta fitar.
Rahoton kasancewa Musulmi a Turai, da aka fitar a ranar Alhamis kuma duba ga alkaluman 2022, ya bayyana kari sosai a nuna kyamar Musulmai, inda kashi 47 na Musulman da aka tambaya suna bayyana fuskantar nuna wariya, kari daga kashi 39 da aka samu a 2016.
Tambayar jama'a da aka yi ta yi karin haske kan daduwar kalubalen da Musulmai ke fuskanta a fadin Turai, musamman wajen samun ayyukan yi da wajen zama.
"A mafi yawancin lokuta Musulmai na fuskantar nuna wariya a lokacinda suke neman ayyukan yi (kashi 39) ko a wajen aiki (kashi 35)," in ji rahoton.
Rahoton ya bayyana cewa wadannan batutuwa na da tasiri a wasu bangarorin, kamar samun gidan zama, ilimi da kula da lafiya.
Rahoton ya kara da cewa mata da ke saka tufafi na addini sun fi fuskantar nuna wariya sama da wadand aba sa saka wa, musamman a loakcin da suke neman aiki, kuma hakan ya karu da kashi 45 a 2022 kari kan kashi 31 a 2016, inda mata masu shekaru 16-24 suka fi fuskantar nuna wariyar da kashi 58.
'Karuwar nuna wariya mai sanya damuwa'
Nuna wariya a bangaren neman gidaje ma ya karu, inda kashi 35 na wadanda aka tambaya suka ce sun kasa samun gidan haya ko na sayarwa saboda nuna wariya, kari sosai sama da kashi 22 da aka samu a 2016.
Rahoton ya kuma haskaka bayanai game da aiwatar da dokoki, inda kusan rabin (kashi 49) wadanda 'yan sanda ke tsayarwa ke fuskantar nuna wariya.
Daraktar FRA, Sirpa Rautio ta bayyana yanayin a matsayin wanda ya ta'azzara, tana mai cewa "Muna shaida karin nuna wariya mai sanya damuwa da ake yi nuna wa Musulmai a Turai."
Ta alakanta wannan ga rikicin Gabas ta Tsakiya da "mummunan dabi'ar nuna wariya ga Musulmai a fadin nahiyar."
"Muna bukatar tabbatar da cewa kowa ya samu sukuni a Turai, an tafi tare da shi, an girmama shi, ba tare da duba ga launin fata, asali ko addininsa ba," in Rautio.