A ranar 16 ga Maris din 2010 Lula ya kai ziyara Yammacin Gabar Kogin Jordan / Hoto: Reuters

A watan Maris din 2010, a lokacin da aka zabe shi shugaban kasa a karon farko, Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ya kai ziyara Isra'ila da Falasdinu wanda a wannan lokacin aka bayyana hakan a matsayin ziyara ta tarihi.

A Majalisar Dokokin Isra'ila, jagoran na Brazil ya bayyana yadda mamayar da Isra'ila ke yi wa yankunan Falasdinawa ta saba wa dokokin kasa da kasa, kuma hakan ke lalata yunkurin zamar da zaman lafiya.

A jawabinsa, a yayin kira da a kafa 'yantacciyar kasar Falasdinu ya bukaci da "A yi tattaunawa tare da kawar da rashin yarda".

Lula ya gana da Shugaban gwamnatin Kasa ta Falasdin (PNA) Mahmoud Abbas da kuma Firaminista Salam Fayyad inda ya dinga fadin "Ina mafarkin ganin an samu 'yantacciyar kasar Falasdinu mai cin gashin kanta da ke zaune lafiya a Gabas ta Tsakiya."

Ya kuma ajiye fure a kabarin marigayi tsohon jagoran Falasdinawa Yasser Arafat. Daga baya Lula ya sanya hannu kan yarjeniyoyi biyar da gwamnatin Falasdin da suka shafi bangarorin ayyukan noma da ilimi da wasanni da lafiya da yawon bude ido.

Ya zuwa Oktoban 2023, bayan sabon rikicin da ya barke tsakanin Hamas da Isra'ila, Lula ya yi kira ga tsagaita wuta nan da take inda ya sake nanata cewa "bai kamata mutanen Gaza da ba su ji ba ba su gani ba su dinga cutuwa saboda haukan wadanda suke son yaki".

Daga wancan lokacin zuwa yau, Lula ya kasance yana kare martabar Falasdinawa ba tare da wani shayi ba, wasu masu nazari sun bi diddigin wannan yunkuri nasa.

A lokacin da ake mulkin kama karya a Barazil, Lula shugaban kungiyar da ke fafutuka saboda hakkokin ma'aikata a Sao Paulo da sauran bangarorin Brazil ya dinga gwagwarmayar ganin an dabbaka dimokuradiyya, in ji Sayid Marcos Tenorio, mataimakin shugaban Cibiyar Barazil-Falasdin (IBRASPAL).

A shekarar 1980, lokacin da Lula ya kafa jam'iyyar Leba, ba yunkurin dabbaka dimokuradiyya kawai ya yi ba, har ma da yakar zaluncin da azzaluman gwamnatoci ke yi ya yi, in ji mai nazari kan harkokin siyasa Marina Pontes.

Tare da kudirin yakar 'yan mulkin mallaka da masu mulkin danniya, ta bayyana yadda Lula ke kallon al'amarin Falasdin a matsayin "Yunkurin nuna goyon baya".

"Daga shekarun 1980, jam'iyyar ta kula alaka a hukumance da Kungiyar Gwagwarmayar 'Yantar da Falasdinawa (PLO), kuma Lula ya kula kyakkyawar dangantaka da shugaban Falasdinawa Yasser Arafat inda suka ana da juna a farkon 1991," Pontes ta shaida wa TRT World.

"Gwagwarmayar gaggawa"

A tsawon shekarun nan, ana yi wa yadda Lula ya rike neman 'yancin Falasdinawa kallo a matsayin "gwagwarmayar gaggawa" a Kudancin Duniya, in ji Guilherme Casaroes, farfesa a Jami'ar Kasuwanci ta Sao Paulo mallakar Asusun Getulio Vargas.

Hakan ya kawo zurfafar jam'iyyar Lula da PLO. A Latin Amurka, ya ce jam'iyyar da sauran jam'yyun adawa na kallon batun Isra'ila da Falasdin a matsayin yaki tsakanin wanda ake zalunta da azzalumi.

Lula ya ci gaba da bayyana ra'ayin samun kasar Falasdinu mai cin gashin kanta. Hoto: Rueters

"Hakan ya tunzura kasashen Latin Amurka, wadanda Turawa suka yi wa mulkin mallaka kuma Amurka take musu mulkin danniya. Amma yana da muhimmanci a ambaci cewa ko a zamanin mulkin kama karya na soji ma (1964-1985) Brazil ta goyi bayan muradin Falasdinawa.

Kuma ta dinga goyon baya warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu, matakin da Lula ya ci gaba da karewa bayan zaman sa shugaban kasa a 2003," in ji Casaroes, yayin tattaunawa da TRT Aworld.

Bayan kama aiki a karon farko, Lula ya yi kokarin mayar da Barazil kasa mai karfin fada a ji da ke tasowa, in Casaroes, kuma wannan mataki ya sanya kasar kulla kakkarfar dangantaka da Gabas ta Tsakiya.

A tsawon shekaru takwas da ya yi a kan mulki, gwamnatin Lula ta bayyana za ta shiga tsakani game da rikicin nukiliyar Iran da ma rikicin Isra'ila da Falasdin.

A zamanin mulkinsa, Lula ya kuma kalubalanci karfin Amurka da ikon da take d ashi kan hukumomin kasashen duniya. "

A wani abu da kwararru suka bayyana da "Nisantar bangarori biyu" a yaki, yunkurin Lula bai bamanta da yadda Brazil ta dinga shiga tsakanin rikice-rikice a baya ba, in ji Casaroes, amma kuma "ta fi zage damtse da nuna ƙaimi" a wannan karon.

Sai dai kuma, Casaroes ya kara da cewa matakan diplomasiyya da matsayin Barazil game da Falasdin a yankin ya bambanta da na sauran gwamnatocin Latin Amurka, kamar Venezuela da Bolivia, wadanda sun ma fi sukar Isra'ila.

A tarihance, kokarin diplomasiyya na Barazil na tsawon shekaru 50 ya bukaci warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu, in ji Andre Luiz Reis da Silva, Mataimakin Farfesa malami a Sashen Nazarin Kasa da Kasa a Jami'ar Tarayya ta Rio Grande do Sul.

Amincewa da kafa kasar Falasdin

Hakan ya yi daidai da al'amura da yawa da suka yi ta faruwa a jere kan wannan manufa "kuma a hukumance ba wai kawai a yi taro a tashi ba", in ji Pontes.

Sun hada da bayar da kyautar fili a Brazil don gina ofishin jakadancin Falasdin, naɗa jakada na musamman, bude ofishin wakilci a Ramallah, ziyara a hukumance sau uku - biyu ta Barazil zuwa Gabas ta Tsakiya, daya kuma ta Abbas zuwa Brazil.

Sannan da gudanar da taron Kasashen Kudancin Amurka da Kasashen Larabawa.

Brazil ta kuma halarci babban taron Annapolis na 2007, Paris 2008 da na Sharm Al SHaikkh a 2009, kuma ta bayar da manyan kyaututtuka guda biyu na kayan magunguna da abinci.

Amincewa da Falasdin da Brazil ta yi ya janyo samun tasiri mai kyau, inda makota irin su Arentina da Bolivia da Ecuador ma suka amince da kafa kasar Falasdin.

Chile da Guyana da Peru da Suriname da Uruguay ma sun bi sahu shekarar da ta gabata.

Lula ya kuma dauki wannan muradi na Falasdinawa zuwa ga fagen kasa da kasa.

Tenerio na tuna yadda, a lokuta takwas daban-daban, bayanan Lula a Zauren Majalisar Dinkin Duniya suka hada da kare muradun Falasdinawa a matsayin "kasa mai 'yanci da cikakken iko".

Ya kuma soki yadda Isra'ila ke zalunta da cusgunawa Falasdinawa.

Brazil a karkashin shugabancin Lula ta bayar da gudunmowa sosai wajen jan hankalin kasashe makota su amince da kafa kasar Falasdinu mai 'yanci. Hoto: Rueters

Sai dai kuma, a karkashin gwamnatin ra'ayin rikau ta jair Bolsanaro daga 2019 zuwa 2022, Brazil ta karkata ga goyon bayan Isra'ila saboda kawnacen addini na cikin gidam in ji Da SIlva.

Hakan ya sanya gwamnatin Bolsanaro bude ofishin kasuwanci a Jerusalem a 2019.

A watan Janairun 2023, Lula ya sake dawowa kujerar shugaban kasa bayan shekaru 13.

Casaroes ya bayyana cewa shugaban ya fuskanci wani sabon yanayi a cikin gida da waje. Ya ga yadda Brazil ta rasa karfin da take da shi a baya, wanda "Ya dogara kan karfin da ake samu ba ta hanyar yaki ba".

Matsin lambar kasashen Yamma

A wannan shekarar, Lula ya fuskanci kalubale daga Yamma bayan da ta bai wa jiragen ruwan Iran shiga iyakarta, sannan da yadda ta ki bai wa Ukraine makamai a yayinda ake yakin Ukraine-Rasha.

Pontes ta ce "Yadda Barazil ba ta shiga yakin ba, ya zama kamar tana nuna goyon baya ga Rasha ne."

Sai dai kuma, a yayin da Yammacin Duniya ke bayar da goyon baya ga Ukraine, amma kuma game da Isra'ila-Falasdin sai lamarin ya zama sabanin na na Ukraine.

Pontes ta kira wannan da "munafurci game da zaluntar Falasdin idan aka kwatanta da yadda suka yi ga Ukraine".

Casaroes ya kuma ce rikicin Isra'ila da Falasdin ya zama mai raba kawuna a harkokin siyasar cikin gida a Brazil.

Bangare daya na kalubalantar mamayar da isra'ila ke yi wa Falasdinawa, suna tirsasawa Lula da ya fito ya soki hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.

"Matsin lamba na cikin gida na iya bayanin me ya sa Lula a karon farko ya bayyana Isra'ila na aikata kisan kare dangi a Gaza.

"Duk da hakan na kusanto da Lula ga masoyansa, amma hakan na nesanta Brazil daga matsayin mai shiga tsakani," in ji Casaroes.

Da Silva na cewa, Barazil ta dauki matakin a dinga yin karba-karba a shugabancin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya inda ta amince kan matakin bayar da kariya ga fararen hula.

Ya ce "Diflomasiyyar Brazil ta bukaci matsayin daidaito da sulhu, girmama tsarinmu na diolomasiyya, amma kuma babu karfin fada a ji ga matsayinta," in ji shi.

A ranar 14 ga Nuwamba, a yayin da Isra'ila ke tsaka da kai hare-hare Gaza, Barazil ta karbi 'yan gudun hihirar Falasdin 32 daga yankin Gaza.

Tana bibiyar hare-haren da suka kashe Falasdinawa sama da 15,000, aka kuma kashe 'yan Isra'ila kimanin 1,200.

A sansanin sojin sama na Barazil da ke babban birnin kasar, inda Lula ya tarbi 'yan Barazil 22 da 'yan uwansu 10, ya zargi Isra'ila da 'kashe mutane ta ci barkatai', ya kuma ce bai taba ganin irin wannan cin zarafi ga dan adam ba a ban kasa.

Da Silva na da ra'ayin cewa hakan "ya janyo raguwar karfin alaka da Isra'ila, duk da cewa an ci gaba da kulla dangantakar diplomasiyya".

A cikin gida, hakan ya janyo suka daga kungiyar Tarayyar Barazil-Isralika (CONIB). Kungiyar d acewa tana wakiltar Yahudawan Brazil 120,000 sun soki kalaman Lula da cewa kalamai ne na "Kuskure da hatsari".

CONIB na ikirari da cewa Isra'ila "ta yi kokarin kare rayukan fararen hula Falasdinawa", kuma ta yi kira da a yi kalamai na daidaito.

Duk wannan korafi na jama'a, Tenorio ya ce Brazil ta ci gaba da nuna halayyar goyon baya ga Falasdin, kuma taba bayyana hakan karara ga duniya.

"Jam''yyun Barazil, kungiyoyin 'yan kasuwa da na kwadago, shahararrun kungiyoyin gwagwarmaya na nuna goyon bayan 'yantuwar Falasdin. Lula na cikin wannan tsari dumu-dumu."

A watan Mayun 2005 shugaban Falasdinawa Abbas ya ziyarci Barazil. Hoto: Rueters
TRT World