Daga Fayha Shalash
Wasu ma'aurata da dama 'yan Falasdinu da zaman gidajen yarin Isra'ila ya raba su, sun koma fasa ƙwaurin maniyyi daga kurkuku domin samun haihuwa da kuma tara iyali.
Sai dai ba abu ne mai sauki a haifi jariri ta hanyar dashen ƙwai musamman ga mata 'yan Falasdinu da sai sun bi tsarin ba tare da mazajensu a kusa da su ba.
Sama da maza Falasdinawa 7,000 ne ke garkame a gidajen yarin Isra'ila bisa wasu tuhume-tuhume da ake yi musu, sannan wasu na fuskantar hukuncin tsawon shekaru ba tare da sassaucin fitowa nan kusa ko kuma a yi musu afuwa ba.
Sannan akwai yiwuwar adadin ya daɗa ƙaruwa sakamakon yadda sojojin Isra'ila ke ci gaba da tsare Falasdinawa maza ba bisa ƙa'ida ba a yakin da ake yi a Gaza.
A tsawon shekaru da dama, Tel Aviv na daukar Falasdinawa daga yankunan da aka mamaye a matsayin marasa gata da 'yanci, lamarin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka kira da mulkin wariyar launin fata na zamani.
Alal misali, an hana Falasdinawa bin hanyoyin da aka keɓe wa Yahudawan Isra'ila.
An sanya wasu tsare-tsaren dokoki kan kadarori daban-daban ga mazauna Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye daga wadanda suka shafi mazauna Isra'ila ba bisa ƙa'ida ba da ke zaune a kusa da juna.
Wata mata Bafalasdiniya 'yar Gaza da ta auri wani mutum dan yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, an tilasta mata renon 'ya'yanta da kanta saboda ba a yarda ta zauna da mijinta a matsayin ma'aurata a Yammacin Kogin Jordan ba.
Isra'ila ba ta yarda a kawo wa fursunonin Falasdinawa ziyara ta auratayya ba, wanda ke zama al'ada a yawancin kasashe masu tsari irin na dimokuradiyya a duniya.
Datse labarin soyayya
A shekarar 2010 ne Renan Al Salhi, wata 'yar Falasdinu mai shekaru 34, ta auri Islam Hamed. Dukkansu biyu sun fito ne daga garin Silwad da ke gabashin Ramallah, yankin da ke karkashin haramtacciyar mamayar Isra'ila. Tana da burin tara iyali.
Amma bayan wasu 'yan watanni, jami'an tsaron Falasdinu suka kama Hamed bisa zargin harbin wata motar 'yan Isra'ila.
Ya shafe shekaru biyar a gidan yarin Falasdinu. A lokacin ne Al Salhi ta haifi ɗansu na farko, namiji, suka sa masa suna Khattab.
Al'amura sun kara muni wa ma'auratan da ba su taba zama tare wuri daya ba, baya da sojojin Isra'ila suka kama Hamed ana sako shi daga gidan yarin Falasdinu a 2015. a yanzu haka yana fuskantar hukuncin shekaru 21.
Samun wani yaro a ko yaushe yana cikin tunanin Al Salhi. Kamar yawancin iyaye mata, tana son ta sama wa danta na fari dan'uwa, sai dai samun hakan na zama abu mai matukar wuya.
Za ta iya tsufar daukar ciki a lokacin da mijinta zai fito daga kurkukun Isra'ila.
Hanya daya tilo ita ce, ko ta yaya ta a samu damar fitar da maniyyin mijin daga gidan yarin don su haifu ta hanyar dashen kwan haihuwa (IVF).
Aika soyayya daga gidan yarin Isra'ila
Bafalasdine na farko da aka haifa wa wani fursunan Isra'ila ta wannan hanya shi ne Muhammad dan Ammar Al Zaben, wani Bafalasdine daga yankin Nablus, wanda ake tsare da shi tun 1998 kana yana fuskantar hukuncin daurin rai da rai.
An gudanar da wannan tsarin dashen kwan haihuwa ne ta hanyar ''fasa kwaurin maniyyi'' a Cibiyar Kula da Lafiyar iyali ta Rezan dake Nablus.
Dokta Jamila Abu Khaizran, wacce ke aiki a cibiyar, ta ce ana bin ka’ida mai tsauri kafin a gudanar da aikin dashen ƙwan.
“Cibiyar ba ta da alhakin yadda ake kawo maniyyin. Amma muna bukatar shaidu daga dangin miji da matar su kasance a wurin idan ya isa cibiyar.”
A shekaru sama da goma tun da aka fara fasa kwaurin maniyyi, an haifi jarirai 120 ta hanyar IVF.
''Ana yanke shawarar karshe ne na amfani da samfurin maniyyi bayan an gudanar da bincike. Idan bai dace da tsarin ba, duk kokarin da aka yi ya baci sai dai kuma a sake neman wani samfurin, "in ji Khaizran.
Dace na samun tagwaye
Hamed dai ya dage duk da cewa Labari ya bazu game da yadda fursunonin Falasdinawan ke fasakwaurin maniyyinsu ba bisa ka'ida ba don tara iyali.
A duk lokacin da Renan ta ziyarce shi a kurkukun Isra'ila, Hamed yakan kawo mata batun, tare da naci kan su kwada.
“Ba abu ne mai sauki ba. Tsarin na da matukar wahala, Ko tunanin yin abin ma yana da gajiyarwa. Sai kuma na yi la’akari da haihuwar da abin da zai faru bayan haka,” in ji Al Salhi.
“Kula da Khattab, dana na fari, da kaina shine abu mafi wahala da na taba yi a rayuwata. Yanzu ya zama dole na yi tunani mai zurfi na samun wani yaro.”
Duk da haka, ma'auratan daga Silwad sun yanke shawarar daukar wannan mataki saboda Hamed ba shi da lokacin fita daga kurkuku da wuri.
Daya daga cikin abokan Hamed daga gidan yarinda aka sako ya kawo maniyyi a cikin wani 'dan kwalba.
Al Salhi ta ce ta yi sa'ar samun juna biyu ba tare da wata matsala ba. A shekarar 2021, ta haifi tagwaye - namiji mai suna Muhammad da yarinya mai suna Khadija.
“Shawarar samun ’ya’ya ta wannan haryar ta karya lagon iIsra’ila, duk yaron da aka haifa ta wannan hanyar shaida ne na cewa gidajen yarin Isra'ila ba za su iya hana rayuwar Falasdinawa ta ci gaba da gudana ba."
Al Salhi ta ce ta yi sa'ar samun tallafin 'yan'uwa da na al'umma, a da'irar masu ra'ayin addini ta mazan jiya, wasu su na iya yi hakan wata mumunar fahimta .
A lokacin da ta je neman a dasa mata kwanta, wasu matan Falasdinawa da dama sun dauki ciki ta wannan hanyar da tuni ya samu karbuwa.
Ko da yake ba duka matan Falasdinawa ke yin sa'a ba.
Ba tafiya ba ce mai sauki
Duk da saukin tsarin dashen, mata da dama ba su yi nasarar samun juna biyu ba.
Iman Saeed, mai shekaru 34, daga Bethlehem, tana da ’ya’ya uku. An kama mijinta a shekarar 2016 kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.
Shekaru uku da kama shi, ya gaya mata burinsa na sake haihuwa. ita ma ta mara masa baya kan hakan. Ya kuma ni sa'ar fitar da maniyyinsa daga gidan yari.
“Na je cibiyoyin kiwon lafiya da yawa, amma wasu daga cikinsu sun ki saboda yawanci ana ba da fifiko ga fursunonin da ba su da yara da kuma matan da suka kusan shekaru 40. A karshe dai, na samu an dashen kuma na yi farin ciki sosai,” in ji ta.
Saeed ta yi jiran tsawon makonni, amma ciki bai shiga ba. Ta sake gwada dashen, amma abin ya ci tura.
“Na shiga cikin damuwa mai tsanani. Yarana kuma sun yi farin ciki a lokacin da na shaida musu za su sami dan’uwa. amma kuma hankalinsu a tashe yake. Muna ta zumudin jiran jaririn kamar wata alama ce ta samun ’yancin mijina,” in ji ta.
Tsarin dashe na IVF na da tsada. wa Saeed, aikin ya kai kusan shekel dubu 25 (fiye da dalar Amurka 7,000), ban da kudin da za a batar wajen haihuwa idan ta zo, wanda a mafi yawan lokuta ake bukatar tiyata ta C-Section.
Wasu wuraren kiwon lafiya suna aikin tsarin dashen kyauta ga matan fursunonin, amma Saeed ta ce, sai iyaye dake nema sun cika sharudda da dama aka gindaya musu, ciki har da cewa fursunar bai taba haihuwa ba ko kuma ba shi da yara.
“Wasu matan sun dauki ciki cikin nasara, amma ɗan tayin ya mutu bayan wasu ‘yan watanni kuma sun ji takaicin hakan. Duk dai abin sa’a ce da yardar Allah.”
Mijinta ya yi mata fasa kwaurin sabbin maniyyi kwanaki kadan kafin barkewar yakin a ranar 7 ga Oktoba, sai dai ba a yi mata dashen ba saboda tana fatan za a sake shi a wata yarjejeniyar musayar fursunoni.
“Kasancewar mijina a tare da ni a lokacin daukar ciki da kuma haihuwa abu ne da na ke matukar muradi sannan burin ko wacce mace. Yanayin da macen da ta haihu ta hanyar fasa kwaurin maniyyi ba ta samu.”
Fayha Shalash yar jaridar Falasdinu ce da ke garin Ramallah. Tana da digiri a aikin jarida na talabijin daga Jami'ar Birzeit. Ta kasance babbar mai ba da gudunmawa ga tashar watsa shirye-shiryen gida tun shekarar 2009, sannan ta rubuta wasu labarai ta kafar gidajen jarida na yanar gizo daban-daban.