Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da hadin gwiwa ta fannin dijital tsakaninta da Saudiyya don samar da tsarin ba da katin lafiya ga Mahajjata, da manufar taimaka wa kusan Musulmai miliyan uku da ke zuwa Aikin Hajji kowacce shekara.
Katin lafiya na Mahajjata, wani tsarin kula da lafiya ne a zamanance, kuma an shigar da shi Tsarin Duba Lafiya na Dijital na WHO, inda za a dinga amfani da kayan asibitocin gwamnati don taƙaita bayanan lafiyar Mahajjata, ciki har da me suke bukata ta fuskar lafiya da gano cuta da matsayin riga-kafi da wasu abubuwan, in ji hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.
Sanarwar ta WHO ta ce matafiya na iya ba da bayanan lafiyarsu ga mahukuntan kiwon lafiya, suna masu tabbatar da cikakkun bayanan mara lafiya, da manufar tabbatar da kula da lafiya yadda ya kamata a lokacin Aikin Hajji.
"Yau ce ranar da aka samu babban cigaba a goyon bayan da WHO ke baiwa kasashe mambobinta wajen fadada samun damar kula da lafiya mai inganci da tsarin mayar da hankali kacokan ga marasa lafiya a duk lokacinda bukatar hakan ta taso," in ji babban jami'in kimiyya na WHO, Jeremy Farrar.
'Hajji Mafi Yawan Jama'a'
"Muna godoya ga cikakken goyon bayan da Masarautar Saudiyya, kasashe mambobi da Ofishin Shiyya na WHO a Gabashin Bahar Rum ke bayarwa, kuma muna sauraren karin goyon bayan aiki tare a kasashe don ganin sun koma aiki da tsarin na zamani wajen kula da lafiyarsu," in ji Farrar.
"Aikin Hajji" shi ne taro mafi yawan jama'a a duniya, inda ake samun Musulmai kusan miliyan uku daga kasashe sama da 180 a kowacce shekara da suke Sauke Farali a Makka na Saudiyya, in ji Hukumar ta WHO.
Sanarwar ta kuma kara da cewa gwajin da aka yi a 2024 ya yi nuni da cewa sabon tsarin ya inganta tsaro da ingancin kula da Mahajjata a yayin da suke gudanar da Ibadar Hajji,