Hukumar Kula da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da sanya ibadar yin bude-baki ta azumin watan Ramadan mai alfarma, a cikin jerin abubuwan tarihi na al’adu.
Kasashen Turkiyya da Azerbaijan da Uzbekistan da Iran ne suka gabatar da bukatar ga Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba.
“Musulmai na yin buda baki (wanda ake kira Iftar ko Eftari ko Iftor) a lokacin faɗuwar rana a cikin watan Ramadan, bayan kammala dukkan hidimomin addini da na ibada,” in ji UNESCO.
Bude-baki, wanda ake yi bayan kiran sallah da faɗuwar rana a cikin watan Ramadan, yana ƙarfafa alaƙa zumunci tsakanin ƴan'uwa da dangi da abokan arziki, da haɓaka sadaka da haɗin kai da taimakon mabuƙata," in ji shi.
Tun ranar Litinin ne kwamitin kula da al'adun gargajiya na gwamnatocin kasa da kasa ya amince da al'adar tsohuwar al'adar.
A kasashen Musulmai da dama, ana fara yin buda baki ta hanyar cin dabino ko shan shayi. Sannan nau'ukan abincin da ake dafawa ya bambanta a kowane yanki.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce "aikin buda baki yawanci ana yada shi ne a cikin iyalai, kuma yara da matasa galibi aka ba su jagorancin shirya kayan abinci na gargajiya".