Da sanyin asubahin 16 ga Oktoba, gwamman sojojin Isra'ila suka kutsa gidan dan jarida mai daukar hoto Bafalasdine Moaz Amarneh a sansanin 'yan gidun hijira na Dheisheh, da ke kudancin Baytullahim, inda suka yi awon gaba da shi zuwa cibiyar tsare mutane.
Kama wannan mutum wani bangare ne na zalunci da gallazawar da sojojon Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a Yammacin Gabar Kogin Jordan, inda suka kara tsaurara kama Falasdinawa tun bayan da Hamas ta kai harin ba zata kan Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba.
Akalla Falasdinawa dubu daya, da suka hada da tsofaffin fursunoni fa 'yan Majalisar Dokoki da ke da alaka da Hamas da masu fafutuka da 'yan jaridu ne suka fuskanci zaluncin sojojin.
Isra'ila na ikirarin mayar da martani ga Hamas da ta kaddamar mata da hari a karkashin hare-haren "Ambaliyar Al Aqsa" inda suka kai hari sansanin sojojin Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba.
Sansanin Dheisheh waje ne da kowa yana da labarin da zai iya bayarwa game da zaluncin Isra'ila.
Moaz ya rasa idonsa a 2019 bayan harsashin da Isra'ila suka harba masa yayin dauko rahoton zanga-zangar zaman lafiya ta nuna adawa ga mamayar Yahudawa a garin Surif, na arewacin Hebron. Wannan ciwo ya yi mummunan tasiri ga lafiyarsa.
Walaa Amarneh, matarsa ta shaida wa TRT World cewa a yayin harin 16 ga Oktoba, sojojin Isra'ila sun kwace wayar Moaz tare da kama shi. Tun wannan lokaci, ta gaza magana da mijinta, wanda sojojin na Isra'ila suka ki su bayyana inda suka kai shi.
Bayan haka, sun samu labari daga lauya cewar an mayar da shi zuwa kurkukun Megiddo, kuma sojoji sun lakada masa dukan tsiya, wanda hakan ya sanya shi rashin lafiya.
Tabaransa da ke taimaka wajen gani shi ma ya karye.
Walaa ta kara da cewa "Moaz na shan wahala tun bayan da ya jikkata a 2019. Yana yawan shan magungunan rage radadi kuma yana bukatar maganin ciwon sukari, wanda ya same shi bayan jin ciwon daga harsashi, amma duk da haka sojojin sun hana shi shan maganinsa."
Walaa na aiki da kamfanin Sadarwa na J Media, wanda sojojin Isra'ila suka rufe bayan an kai wa Zirin Gaza harin bam.
Harin sojojin da kama Moaz daga baya da aka yi ya janyo damuwa ga yaransa su uku, wadanda suka shaida yadda sojojin Isra'ila suka tafi da mahaifinsu bayan daure hannayensa ta baya, tare da rufe masa idanuwansa.
"Dare ne mummuna. Ban san me ya sa aka kama shi ba, me ya sa suka tsorata yarana tare da farkar da su daga bacci ta hanyar buga kofa da karfi. Har yanzu ina kokarin kwantar musu da hankali, amma a ko yaushe suna tambayar ina babansu," in ji Walaa.
Fuskantar gallazawa a tsare
A yayin da Isra'ila ke batun 'yan kama guri zauna da mayakan Hamas ke rike da su, ita ma ta yi irin wannan abu na kama Falasdinawa ma da yara kanana daga gidajensu tana azabtar da su a wuraren da ta tsare su.
A kauyen Beit Liqya, yammacin Ramallah, sojojin Isra'ila sun kutsa kai gidan mai bincike Najib Mafarja, A yayin da ba su same shi a gida ba, sai suka kama ɗansa mai shekaru uku tare da tsare shi na tsawon awanni biyu, don takurawa babansa ya mika wuya.
Yaron ya dawo gida yana karkarwa cikin firgici da tsoro.
Tsare iyalai don matsawa maza manyan Falasdinawa su mika kawunansu ga sojojn Isra'ila ya zama wani abu na kullum a Yammacin Gabar Kogin Jordan.
Tsohuwar fursuna Bushra al Taweel daga garin Al-Bireh a tsakiyar Yammacin Gabar Kogin Jordan da ke karkashin mamaya tai ce sojojin Isra'ila sun kutsa kai gidanta da asuba a ranar 19 ga Oktoba inda suka hargitsa kayayyakin ciki.
Harin na da manufar kama mahaifinta mai shekara 61, tsohon fursuna Jamal al Taweel, wanda aka saka kasa da shekara guda da ta wuce bayan kwashe shekaru biyu a gidan kurkukun Isra'ila.
An kama shi sau 12 tare da tura shi gidajen kurkukun Isra'ila daban-daban. A jimlace ya yi shekara 16 a kurkuku.
"Mahaifina ba ya nan, sai suka kama 'yan uwana don takura masa ya miƙa wuya,' in ji ta.
Awanni bayan kama su, an saki 'yan uwan nata Nasrallah da Yahya. An zalunci dukkan su a jikkunansu, har da kafa zuwa kai inda ake iya ganin ciwuka da alamar duka. Nan da nan iyalinsu suka kai su asibiti.
Manufa da ta dade
A yayin da hare-haren bam na isra'ila suka kashe Falasdinawa sama da 6,546, da suka hada da yara kanana 2,704 tun daga 7 ga Oktoba, lamarin na kara munana a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye na tsawon shekaru.
Yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da mahukuntan Falasdin ke kula da shi, na yawan fuskantar hari daga sojojin Isra'ila da Yahudawa 'yan kama guri zauna da suke hantara da kashe Falasdinawa.
Yahudawan 'yan kama guri zauna na kwace gonakin Falasdinawa suna mayar da su karkashin Isra'ila ba ko kunya.
Tun daga farkon wannan shekarar har zuwa 7 ga Oktoba, Yahudawa 'yan kama guri zauna sun harbe Falasdinawa 223, kuma an kama dama da dubu biyar a Yammacin Gabar Kogin Jordan.
Mai nazari da warwarar al'muran yau da kullum Bafalasdine Sari Orabi ya shaida wa TRT World cewa Isra'ila na yawan neman mafaka ta siyasa daga shugabannin Yammacin duniya don kashe Falasdinawa da rushe dukkan gine-ginensu da ke Zirin Gaza.
Orabi ya ce "Isra'ila na cewa dalilin da ya sanya duk wannan shi ne farmakan Ambaliyar Al Aqsa, amma ta san duniya ba za ta aminta da wannan abu , inda za su fi karkakata ga tausaya wa Falasdinawa.
Ya kara da cewa wadannan hare-hare a kan Masallacin Ƙudus da zaluntar Falasdinawa fursunoni da kisan marasa ƙarfi a kowacce rana da sauran ayyukan rashin adalci su ne suka harzuƙa Hamas kai wadannan hare-haren na ranar 7 ga watan Oktoba.
Ya kara da cewa "Isra'ila ba ta son a tattauna me ya janyo wannan rikici, amma tana son ta samu mafaka ta musamman don kashe Falasdinawa."