'Mutane da dama sun mutu a hari na biyu da Isra'ila ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia a Gaza

'Mutane da dama sun mutu a hari na biyu da Isra'ila ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia a Gaza

Ƙungiyar Hamas ta ce an kashe mutum bakwai daga cikin mutanen da take garkuwa da su, ciki har da wasu uku masu fasfunan ƙasashen waje a harin.
Ma'aikatar Lafiya ta yankin ta ce fiye da mutum 50 aka kashe a harin ranar Talata. / Photo: Reuters

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ce Isra'ila ta sake kai wani harin bam sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia, wanda shi ne mafi girma a birnin, inda gomman mutane suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata.

Ta ce "akwai shahidai da dama da wadanda suka ji raunuka sakamakon hare-haren jiragen mamayar Isra'ila" a sansanin gudun hijira na Jabalia a ranar Laraba, kwana ɗaya bayan da Isra'ila ta kai mummunan hari wannan wajen.

Masu aikin ceto sun ce "an kashe illahirin iyalai", amma ba za a iya bayar da cikakken bayani a kan ɓarnar da aka samu ba. Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba.

Ma'aikatar Lafiya ta yankin ta ce fiye da mutum 50 aka kashe a harin ranar Talata.

Ƙungiyar Hamas ta ce an kashe mutum bakwai daga cikin mutanen da take garkuwa da su, ciki har da wasu uku masu fasfunan ƙasashen waje a harin.

Bala'i na baya-bayan nan

Shugaban Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Griffiths ya soki harin da aka kai wa Jabalia bayan wata ziyara ta kwanaki biyu da ya kai Isra’ila da yankunan Falasdinawa da aka mamaye.

A wata sanarwa da ya fitar, Griffiths ya ce “Wannan ce musiba ta baya-bayan nan da ta afka wa mutanen Gaza inda rikici ya shiga mataki mai firgitarwa, kuma hakan ya janyo ake samun wahalar gudanar da ayyukan jinkai.”

Ya ce “Kamar duniya ta gaza yin komai, ko ba ta son ta yi wani abu,” inda ya kuma kara da cewa “Ba za a ci gaba da wannan ba. Muna bukatar daukar matakan sauyi.”

Griffiths ya kuma ce “Muna bukatar bangarorin da ke rikici da juna su yarda su dakatar da yakin” ta yadda za a kai kayan taimakon gaggawa zuwa ga Falasdinawa miliyan 2.4.

A ranar Talatar nan Isra’ila ta bayyana cewa a harin da ta kai ta kashe wani babban kwamandan Hamas a Jabalia, Ibrahim Biari “wanda na daya daga cikin wadanda suka kitsa harin 7 ga Oktoba.”

Isra’ila ta kuma kara da cewa an kashe mutane 1,400 mafi yawan su farar hula tare da kama wasu 240 a hare-haren da Hamas ta kai.

Tuni ta kaddamar hare-hare ta sama, kasa da ruwa a kowacce rana wanda hakan ya yi ajalin Falasdinawa 8,700 da suka hada da yara kanana sama da 6,000.

TRT World