Isra’ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AA

0531 GMT — Marasa lafiya 270 sun fice daga Asibitin European na Gaza

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce marasa lafiya 270 sun fice daga Asibitin European na Gaza da ke Khan Younis bayan wani umarni da Isra’ila ta bayar na ficewa daga Khan Younis.

Richard Peeperkorn, wanda shi ne wakilin WHO a yankunan Falasɗinu da Isra’ila ta mamaye ya shaida wa wani taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva cewa odar da Isra’ila ta bayar ta baya-bayan nan na da tasiri matuƙa kan ayyukan da ake yi a Asibitin European Gaza, duk da cewa ba asibitin ba ya cikin wanda aka bayar da odar kan cewa a fice daga ciki.

Isra’ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza waɗanda akasarinsu mata ne da yara.

0957 GMT — Harin sama na Isra'ila ya kashe Falasɗinawa 10 a wata kasuwa a Gaza

Wani harin sama da Isra'ila ta kai kan wata kasuwa a kudu maso gabashin Gaza ya hallaka Falasɗinawa 10 da jikkata wasu da dama

Wasu majiyoyin lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Turkiyya na Anadolu cewa "An kai gawar mutum 10 da waɗanda suka jikkata da dama asibitin al-Ahli Baptist sakamakon harin saman da Isra'ila ta kai unguwar Zeitoun.

Wani jirgin yaƙin Isra'ila ne ya kai harin wata kasuwa mai cunkuso da ke kusa da Masallacin Shama'a a unguwar Zeitoun, lamarin da ya jawo mace-mace da jikkata, kamar yadda shaidu suka shaida wa Anadolu.

1132 GMT — Aƙalla Falasɗinawa 25 Isra’ila ta kashe a hare-haren baya-bayan nan da ta kai a Zirin Gaza, wanda hakan ya jawo adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a Falasɗinu ya kai 37,925 tun daga 7 ga Oktoba, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana a ranar Talata.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce zuwa yanzu mutum 87,141 ne suka jikkata tun bayan soma yaƙin.

“Sojojin Isra’ila sun kashe mutum 25 da jikkata 81 a jerin ‘kisan kiyashi’ uku da suka gadanar a kan wasu iyalai a sa’o’i 24,” in ji ma’aikatar.

0726 GMT — Daraktan Asibitin al-Shifa na Birnin Gaza ya ce Falasɗinawa da dama da ke gidajen yarin Isra'ila sun mutu sakamakon azabtarwa da rashin samun kulawar likitoci da hana su magunguna idan ba su da lafiya.

Ya ƙara da cewa likitoci da ma'aikatan jinya na Isra'ila na cikin mutanen da suke wulaƙantawa tare da azabtar da Falasɗinawa fursunoni ta hanyar hana su magungunan da suk kamata su yi amfani da su idan ba su da lafiya.

Ya ce ana azabtar da Falasɗinawa ta hanyar lakaɗa musu duka da kuma ba su abinci ƙalilan.

"Fursunoni 'yan asalin Gaza sun rame sosai inda suka ragu da kimanin kilogiram 25 na nauyin da suke da shi saboda rashin abinci," in ji Dr. Abu Salmiya.

0417 GMT — Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin ƙaurace wasu yankuna masu yawan jama'a.

Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka hallaka mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, cewar wata majiyar lafiya da kuma ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinawa.

Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis. / Hoto: AA

0414 GMT — Australia ta dakatar da 'yar majalisa saboda goyon bayan ƙasar Falasɗinu

Sanata Fatima Payman ta Jam'iyyar Labor Party ta ce matakin da Firaministan Australia ya ɗauka na dakatar da ita daga kwamitin jam'iyyar ba tare da ƙaidi ba, ya sanya ta zama cikin yanayin "gudun hijira".

Sanata Payman, wadda ke fuskantar dakatarwa bayan ta goyi bayan ƙudurin majalisa na amincewa da ƙasar Falasɗinu, ta ce ta rasa duk wata mu'amala da 'yan kwamitin, cewar rahoton SBS News.

Ta ce an ware ta daga taronsu, da kwamitoci, da tattaunawar kwamitin da samun labarai daga kwamitin.

0308 GMT — Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta kai hari kan jiragen ruwa masu alaƙa da Isra'ila, Amurka, Burtaniya

Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta sanar cewa ta ƙaddamar da harin soji kan jiragen ruwa a Bahar Maliya, da tekun Arabian da Bahar Rum da Tekun Indian Ocean, sadaukarwa ga Falasɗinawa a Gaza.

A wata sanarwa, kakakin sojin ƙungiyar, Yahya Saree ya ce mayaƙansu sun hari jiragen ruwa "masu alaƙa da Isra'ila, Amurka, Burtaniya da Isra'ila” ta amfani da makamai masu linzami kuma harin ya yi nasarar kai wa ga jiragen.

Ta yi nun da cewa ta kai hari kan jirgin ruwan Isra'ila MSC Unific a tekun Arabian Sea, da jirgin dakon mai na Amurka Delonix, a Bahar Maliya, da jirgin Burtaniya “Anvil Point”, a tekun Indian Ocean, da jirgin Lucky Sailor, a Bahar Rum, ba tare da fayyace ƙasar da abin ya shafa ba.

0227 GMT — Marasa lafiya na tserewa daga asibitin Khan Younis kafin Isra'ila ta sake afka masa

Jami'an lafiya da na gudanarwa sun fara kwashe marasa lafiya daga asibitin European Hospital da ke Gaza a birnin Khan Younis gabanin yiwuwar Isra'ila ta sake kai farmaki yankin.

Jami'an na lafiya sun fara kwashe marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni da kuma kayan aikin kula da lafiya saboda asibitin yana cikin yankin da mazaunansa suka samu saƙonnin Isra'ila tana ba su wa'adi da su fice zuwa wani wajen.

Majiyoyin lafiya sun shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Anadolu Agency cewa jami'an lafiya sun kwashe mutane da dama zuwa asibitin Naseer a tsakiyar Khan Younis.

Sun ƙara da cewa su ma jami'an gudanarwar asibitin sun kwashe wasu kayan kula da lafiya saboda tsoron za a lalata su idan Isra'ila ta kai hari asibitin.

Wani wakilin Anadolu ya ba da rahoton cewa su ma mutanen da yaƙi ya raba da gidajensu suna cire tantunansu a kusa da asibitin suna komawa wasu wuraren, bayan samun barazanar farmakin Isra'ila.

Majiyoyin lafiya sun shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Anadolu Agency cewa jami'an lafiya sun kwashe mutane da dama zuwa asibitin Naseer a tsakiyar Khan Younis./ Hoto: AFP
TRT Afrika da abokan hulda