Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya halarci Taron Tsaro na Istanbul wanda Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Kasa ya shirya. / Hoto: AA

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya tuna da Ranar 'Yan Jarida da ke Bakin Aiki, inda ya bayyana cewa dole ne a rika fadin gaskiya a kafafen yada labarai, idan har ana son a samu duniya mai walwala da zaman lafiya.

A wata sanarwa da Sashen Sadarwar ya fitar a ranar Laraba, Altun ya jaddada cewa "daya daga cikin manyan matsalolin duniya a yau shi ne 'Rikicin Fadin Gaskiya' inda labaran karya suka zama babban kalubale a fadin duniya.

Ya ce duk da cewa ana samun karin damarmakin sadarwa a kowacce rana da yadda ake samun bayanai cikin sauki, akwai babbar bukatar samun sahihan bayanai tsantsa kuma a cikin sauki.

Altun ya kara da cewa "Ya kamata a girmama tare da jinjina wa duk 'yan jaridar da ke aiki da ka'idojin fadar gaskiya na aikin jarida, sannan a amince da su a matsayin masu sana'a mai daraja a idon duniya."

"Muna duba tabbatar da fadar gaskiya a kafafen yada labaran da ke kasarmu da ma fagen kasa da kasa a matsayin daya daga cikin jigogin samun zaman lafiya da walwala a duniya."

'Yan jarida a yankin Gaza na Falasdinu

Daraktan Sadarwar ya kuma yi addu'a ga 'yan jaridar da suka rasa rayukansu a yayin da suka tsaka da aiki, musamman a Gaza.

"Abin takaici, rikicin Gaza da aka fara tun 7 ga Oktoba na bayyana 'yan jarida, da ke aiki mai hatsari ga dan'adam, ba sa samun hakkinsu na rayuwa, ballantana a yi maganar hakkin fadin albarkacin baki, ko na karbar bayanai," in ji Altun yayin da yake sukar hare-haren Isra'ila.

Sama da 'yan jarida 100 Isra'ila ta kashe, sannan ta jikkata wasu da dama a hare-haren da take kaiwa yankin Falasdinu da aka yi wa kawanya.

Ya sha alwashin cewa sashen sadarwar zai ci gaba da kare hakkoki da dokokin da suka shafi 'yan jarida, kare rayukansu, da taimaka musu a yayin da suke tsaka da aiki.

Altun ya ce "Ina taya murnar '10 ga Janairu Ranar 'Yan Jarida da ke Aiki' da dukkan ma'aikatan kafafen yada labarai da ke aiki dare da rana suna sadaukarwa, suna yunkurin yin aikinsu da gaskiya da amana, kuma ba sa yadda su kauce hanyar gaskiya."

TRT World